Kocin Arsenal Mikel Arteta na shirin cimma wata babbar nasara a tarihinsa na horar da ‘yan wasan kwallon kafa yayin da zai jagoranci wasansa na 200 a gasar Firimiya a wasan da zasu buga da Manchester United da karfe 5:30 na yamma (agogon Nijeriya) ranar Lahadi.
A wasan ne kuma Arteta ke fatan ganin ya kafa tarihin doke Manchester United gida da waje a kakar wasa daya a Old Trafford a karon farko tun shekarar 1979 kuma Arsenal ta kafa tarihin zama kungiya ta farko da ta lashe wasanni biyar a jere tsakaninta da Man Utd a tarihin gasar Firimiya.
- Ban Ji Dadin Zaman PSG Ba, Messi
- Ban Bar PDP Ba, Ina Gangamin Hadin Gwiwa Ne Don Tunkarar APC A 2027 – Atiku
Wasan da za a yi a Old Trafford zai baiwa kungiyar ta Arteta damar kara nuna wata bajinta bayan nasarar da ta samu a kan PSV Eindhoven da ci 7-1 a tsakiyar mako, duk da cewa United ta tashi kunnen doki 1-1 da Real Sociedad a gasar cin kofin Europa, kungiyar da Ruben Amorim ke jagoranta ta yi fama da rashin nasara a wasanninta na gida a bana.
A wajen Arteta, wasan na ranar Lahadi a gidan Manchester United ba kawai wasa ne na samun maki uku ba, har ma game da bikinshi na wasa 200 a matsayin kocin Arsenal a gasar Firimiya, kocin dan kasar Sifaniya zai shiga cikin jerin jiga-jigan masu horarwa da su ka samu wannan nasara, inda ya zama na 13 kacal da ya yi hakan da kulob guda.