Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tunibu ya ba da tabbacin cewa za su canza salon Yaƙin da hukumomin tsaron Nijeriya ke yi da ‘yan ta’adda da suka hana zaman lafiya.
Bola Ahmad Tunibu ya bayyana haka a lokacin taron neman mafita da gwamnonin arewa maso yamma da hukumar UNDP suka shirya a Katsina.
- Masu Sana’ar Bola-jari Sun Buƙaci Gwamnatin Nijeriya Ta Tallafa Musu Da Rancen Kuɗaɗe
- Shugaban Ƙasa Bola Tinubu Ya Yi Sabon Naɗi A Hukumar Kula Da Ƴansanda
Shugaban wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Kashim Shattima ya bayyana mahimmancin taro iri wannan, ya ce zai taimaka matuƙa gaya wajen samar da zaman lafiya a yankin arewa maso yamma
Haka kuma ya bayyana cewa a wannan karon ya zama wajibi a yi amfani da wasu dabaru da hanyoyi na cikin gida domin shawo kan wannan matsala musamman a arewacin Nigeriya.
“Ta ɓangaren gwamnatin tarayya za mu ƙara ƙarfafa hanyar samar da aikin yi ga matasa da ƙoƙarin inganta zaman lafiya a tsakanin al’umma ta hanyar tattaunawa tare da zuba jari wajen samarwa da matasa aikin yi” inji shi
Ya ƙara da cewa matakan da ake ɗauka za su da ce da ƙoƙarin da jami’an tsaro ke yi wajen samar da zaman lafiya musamman amfani da fasahar zamani wajen yaƙi da ‘yan ta’adda da suka hana zaman lafiya.
Kazalika mataimakin shugaban kasar ya ce gwamnatin tarayya ta warewa shirin nan na Pulako da sai sake ginawa al’ummomin hanyoyi da makarantu da asibitoci da sauran kayayyakin more rayuwa kaso mai tsoka.
A cewar sa, za a fara wannan aikin a jihohin Sakkwato da Kebbi da Katsina da Kaduna da Niger da Bunue a matsayin matakin farko wanda ake sa ran farawa a makonni masu zuwa.
Tuni gwamnatin tarayya ta ware naira biliyan 51 domin fara aikin wanda ake sa ran sai sake gina rayuwar waɗanda bala’in ‘yan bindiga ya shafa.