Shugabar kungiyar Mata Daktoci ta jihar Kaduna kuma ta Kasa (Mai jiran gado), MWAN, Dr. Zainab Muhammad Idris Kwaru ta bayyana cewa, Kungiyar a karkashin jagorancinta za ta maida hankali wajen yaki da ta’ammuli da miyagun kwayoyi ta hanyar hadin guiwa da hukumomin da lamarin ya shafa.
Dr. Kwaru, ta bayyana hakan ne yayin da kungiyar ta kai ziyarar girmamawa ga Mataimakiyar Gwamna Jihar Kaduna, Dr. Hadiza Balarabe Sabuwa a dakin taro da ke gidan gwamnatin jihar a ranar Alhamis 30 ga watan Nuwamba 2023.
Tun da farko, Dr. Hadiza Balarabe sabuwa ta nuna farin cikinta na yadda kungiyar ta girmamata ta kawo mata ziyara har gidan Gwamnatin, inda ta ce, itama Mamba ce a kungiyar ta MWAN.
“Babban abinda nafi son kungiyarmu ta mayar da hankali shi ne, la’akari da yadda za a dakile yawaitar ta’ammuli da miyagun kwayoyi a tsakanin ‘yan mata da yaranmu.
“Ya dace, mu kara fadada tunaninmu ta hanyar hadin guiwa da hukumomin da suka dace, kamar NDLEA, don shawo kan wannan kalubale. Hatsari ne babba cikin al’umma, mace tana shaye-shaye, sabida itace uwa mai tarbiyyantar da ‘ya’yanta da al’umma.” Inji Dr. Balarabe.
A nata jawabin, Dr. Zainab Muhammad Kwaru, ta bayyana cewa, Makasudin ziyarar kungiyar itace, kawo gaisuwa ga mai girma mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Dr. Hadiza Balarabe sabuwa sannan kuma mu bayyana mata nasarar da muka samu, na zabenmu a matsayin shugabar kungiyar mata daktoci ta kasa, kuma mu nuna mata mun yaba da gudunmawar da ta ba mu na daga lokutanta da kudade da muka yi amfani da su na ganin mun samu wannan nasarar.
Daga nan ne, Dr. Kwaru ta zayyana wa manema labarai wasu daga cikin muhimman shirye-shiryen da kungiyar ke gudanarwa a baya da wadanda take kokarin shiryawa a nan gaba, inda tace, sun hada da shiga cikin al’umma mu bada gudunmawarmu na duba lafiya da basu kulawa na musamman, idan har akwai bukatar tura su manyan asibiti, sai mu yi hakan.
Akwai asibitoci na unguwanni da muka sa mambobinmu suna ziyarta don bada gudunmawa na duba marasa lafiya, muna fadakarwa da wayar da kai acikin al’umma daga bangaren kiwon lafiyar Yara da Mata masu juna-biyu. Wasu lokuta, muna kai kayayyakin agaji ga gidajen kaso ko na gajiyayyu ko na Marayu.
Da take mayar da martani kan batun Mataimakiyar Gwamna na dakile yawaitar ta’ammuli da miyagun kwayoyi a tsakanin yara Mata, Dr. Zainab ta bayyana cewa, daga bangarensu, suna amfani da mambobinsu da ke da kwarewa a fannin kwakwalwa, suna fadakarwa da wayar da kai kan illar ta’ammuli da miyagun kwayoyi.
Ta bayyana cewa, akwai damuwa matuka ganin yadda yara Mata yanzun ke ta’ammuli da miyagun kwayoyi, ganin cewa, itace uwa mai tarbiyyantar da ‘ya’yanta da al’umma baki daya. Lallai wannan barazana ce babba acikin al’ummarmu.