Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da inganta karatun Alkur’ani tare da daidaita shi da tsarin ilimin zamani.
Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin rufe gasar karatun Alkur’ani ta jihar karo na 40 da aka gudanar a zauren Sir Ahmadu Bello da ke Dutse, babban birnin jihar. Gwamnan ya bayyana ɗaliban Alkur’ani a matsayin “babbar albarka” ga jihar, yana mai jaddada cewa ilimin Alƙur’ani na taka muhimmiyar rawa wajen gyaran hali da bunƙasa rayuwa.
- Babban Al’amari Ne A Samu Ƴar Shekara 6 Ta Haddace Qur’ani A Makarantar Raudatul Jannah – Mai Sikeli
- ‘Yan Watanni Bayan Shigarsa Musulunci Ya Rubuta Al-Qur’ani Da Hannu A Garin Birnin Gwari
Namadi ya ce bambancin ƙuri’u tsakanin waɗanda suka lashe gasar da sauran mahalarta ya nuna ƙwarewa da ƙwazon da matasan suka nuna. Ya kuma sha alwashin cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa karatun Alƙur’ani ta hanyar hukumar tsangaya, wadda ta haɗa ilimin Alƙur’ani da tsarin ilimin boko tare da kasafin kuɗi na musamman.
Ya ƙara da cewa gwamnati za ta ɗauki nauyin ɗalibai masu ƙwarewa don ci gaba da karatu, ko dai a fannin ilimin Alƙur’ani ko kuma a fannoni na zamani irin su injiniya da likitanci. Haka kuma, ya bayyana cewa jihar ta samu damar karɓar baƙuncin gasar karatun Alƙur’ani ta ƙasa a shekarar 2026, bayan nasarar da ta samu wajen shirya gasar ƙasa da ƙasa da aka kawo daga Limamin Madinah.
Gasar ta bana ta 2025 ta haɗa da mahalarta maza da mata daga sassa daban-daban, inda aka rarraba su kan ɓangarori na karatun hizibi biyu, da goma, da talatin da kuma sittin na Alƙur’ani mai girma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp