Ministan shari’a kuma babban lauyan Tarayya, Lateef Fagbemi (SAN), ya ce Gwamnatin Tarayya ta kuduri aniyar kawo karshen yadda kotunan ke yin hukunce-hukunce masu karo da juna.
Ministan ya bayyana haka ne a ranar Talata a Ilori wajen bude taron kwana uku na kawo sauye-sauye a harkokin shari’a a Nijeriya.
- Kasar Sin: Ya Kamata Nahiyar Turai Ta Girmama Manufar Kasar Sin Daya Tak A Duniya
- Jami’in Yada Labarai: Kasar Sin A Shirye Take Ta Aiwatar Da Hadin Gwiwar Kasashe Na Hakika Tare Da Mambobin G20
Ma’aikatar shari’a ta kasa tare da taimakon Kungiyar Tarayyar Turai ne ta shgirya taron.
Mista Fagbemi, ya ce sabon alkalin alkalan Nijeriya a shirye yake ya bayar da hadin kai wajen yin wannan gyara.
Kuma ya ce shugabancin kungiyar lauyoyi ta Nijeriya, ya nuna cewa lallai akwai bukatar kawo karshen matsalar.
Fagbemi, ya ce sauye-sauyen da ake matukar bukata a bangaren shari’a suna da muhimmanci sosai ga tsari da shirye-shiryen gwamnatin yanzu na bunkasa Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp