Ministan Lantarki, Bayo Adelabu, ya yi barazanar kwace lasisin kamfanonin rarraba wuta na Discos, yana mai cewa ba za a lamunci yanayin da suke saka mutane na karancin wutar ba.
Ministan, wanda ya wallafa sakon barazanar a shafinsa na X a ranar Laraba.
- NiMet Ta Yi Hasashen Bullar Zazzabin Cizon Sauro A Watan Maris Da Afrilu
- Sin Da Aljeriya Na Fatan Bunkasa Hadin Gwiwar Raya Tattalin Arziki
Ya ce ya damu matuka da tabarbarewar samar da wuta da ake fama da rashin ta a fadin kasar nan.
“Don haka ne ma na kira shugabannin Kamfanin Rarraba Lantarki na Abuja (AEDC) da na Ibadan (IBEDC), da kuma shugaban Kamfanin Samar da Lantarki na Nijeriya TCN don yin wata ganawa mai muhimmanci,” in ji ministan.
Ya ce ya kira taron ne don tattaunawa kan yadda ake matukar fama da matsalar samun wuta a wadannan yankunan da kuma nemo mafita.
Yanzu haka dai ana matukar fama da karancin wuta a wasu sassan Nijeriya, musamman babban birnin tarayya, Abuja a daidai lokacin da yanayin zafi ke kara kunno kai.
“Abin takaici ne ganin yadda ake samun raguwar wutar lantarki duk da kokarin da ake yi na inganta lamarin.
“Ma’aikatar Lantarki ta matsa lamba kan Kamfanonin da ke Samar da Wutar (GENCOs) don inganta ayyukansu, lamarin da ya sa aka samu karuwar samar da wuta zuwa sama da megawat 4000,” a cewar Ministan.
Sai dai Mista Adelabu ya bayyana cewa duk da wannan ci gaba da ake samu, wasu kamfanonin sun gaza rarraba wutar da TCN ke bayarwa yadda ya kamata.
Ya kuma koka kan yadda yawan barnar kayayyakin samar da wutar da ake yi ke kara ta’azzara matsalar a Abuja da Benin da Fatakwal da kuma Ibadan.
Minista Adelabu ya sha alwashin cewa daga yanzu zai kama dukkan kamfanonin rarraba wutar da alhaki idan har ba su yi abin da ya dace ba.