Dangane da hukuncin kotun daukaka kara da ta tabbatar da tsige gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da kotun sauraron kararrakin zabe ta yi, jam’iyyar NNPP, ta bayyana aniyar ta na daukaka kara zuwa kotun koli.
Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja a ranar Juma’a ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe, inda ta bayyana dan takarar jam’iyyar APC, Nasiru Gawuna, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 1,127, Sun Sace 518 A Watan Oktoba – Rahoto
- Yadda Za A Sake Farawa Daga Birnin San Francisco
Sai dai Hashimu Dungurawa, shugaban jam’iyyar NNPP na Jihar Kano, ya bayyana rashin gamsuwar jam’iyyar da hukuncin, inda ya jaddada aniyarsu na tafiya zuwa kotun koli.
Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin da kotun baya ta yi, na tsige Abba Kabir Yusuf, inda ta bayyana cewa ba dan jam’iyyar NNPP ba ne a lokacin zabe, wanda hakan ya sa bai cancanci tsayawa takara ba.
Sai dai Hashimu Dungurawa ya musanta wannan hujja inda ya ce za su ci gaba da shari’ar a kotun koli domin tabbatar da hakkin mutanen Kano.
Dungurawa ya bayyana irin rawar da hukumar zabe ta kasa (INEC) ke takawa a matsayin hukumar da ke da alhakin bayyana ko kuma karbar ‘yan takara, inda ya ce shiga lamarin da kotu ke yi a irin wadannan batutuwa bai dace ba.