Tsofaffin Daliban Sashen Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe na Jami’ar Bayero ‘yan ajin shekarar karatu ta 2011 zuwa 2015 sun sha alwashin sabanta dakin karatu na sashen wanda aka fi sani da Dakin Karatu Na Farfesa MKM Galadanci.
Shugaban tawagar tsofaffin daliban, Alh. Hassan Baita Ubawaru, ne ya bayyana haka yayin da yake mika wasu sabbin injinan nadar takardu (Photocopy) guda uku da ya gwangwaje sashen nasu a madadin daliban a matsayin gudunmawarsu don saukaka harkokin koyo da koyarwa a sashen a ranar Alhamis 02, ga watan Nuwambar 2023.
- Jami’ar Bayero Ta Sanar Da Ranar Bude Makaranta Don Ci Gaba Da Karatu
- Tsohon Shugaban Jam’iar Bayero Ta Kano, Farfesa Ibrahim Umar Ya Rasu
Da yake mika injinan, Alh. Hassan Baita, wanda shi ne shugaban taron sada zumunci na ‘yan ajin shekarar 2015 kuma wanda ya dauki nauyan sayan injinan ya ce, wannan somun-tabi ne kuma lokaci bayan lokaci za a ke irin wadannan ayyuka don bunkasa wannan sashe.
A nasa jawabin, tsohon Sakataren Kungiyar Hausa ta Jami’ar Bayero, Muhammad Bashir Amin, ya bayyana kudurinsu na bunkasa sashen ta hanyar bijiro da ayyukan da za su ciyar da sashen gaba, ya kuma bukaci malamai da su kara kyautata alakarsu da dalibansu su ja su a jika, su dauke su tamkar ‘ya’yan da suka haifa, saboda hakan zai kara yi wa daliban kaimi wajen tunawa da su bayan Allah ya daukaka su a rayuwa.
Shugaban Sashen, Farfesa Isah Mukhtar, ya godewa daliban da suka yi wannan hobbasa da abun arziki a lokacin da yake shugabantar sashen, ya kuma bayyana cewa hakika irin wannan tallafi zai taimaka musu su tsallake tantancewar hukumar kula da Jami’o’i ta kasa da za ta yi wa sashen a shekara mai zuwa, wanda gaza samar da kayan koyo da koyarwa da kayan gudanar da aiki ka iya kaiwa ga samun babbar matsalar da zata iya kaiwa ga rufe sashen bakidaya.
Taron ya samu halartar mataimakin shugaban tsangayar fasaha da nazarin addinin musulunci da malaman sashen yayin bikin mika injinan.
Mahalarta taron daga bangaren malamai da dalibai sun jinjinawa kokarin tsofaffin daliban na samar da injinan, sun kuma gode musu da fatan Allah ya yalwata arzikinsu.