Tsofaffin Ɗaliban Sashen Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe na Jami’ar Bayero ‘yan ajin shekarar karatu ta 2011 zuwa 2015 sun sha alwashin sabunta ɗakin karatu na sashen wanda aka fi sani da Ɗakin Karatu Na Farfesa MAZ Sani.
Shugaban tawagar tsofaffin ɗaliban, Alh. Hassan Baita Ubawaru, ne ya bayyana haka yayin da ya ke miƙa wasu sababbin injinan naɗar takardu (Photocopy) guda uku da ya gwangwaje sashen nasu a madadin ɗaliban a matsayin gudunmawarsu don sauƙaƙa harkokin koyo da koyarwa a sashen a ranar Alhamis 02, ga watan Nuwambar 2023.
- Jami’ar Bayero Ta Sanar Da Ranar Bude Makaranta Don Ci Gaba Da Karatu
- Tsohon Shugaban Jam’iar Bayero Ta Kano, Farfesa Ibrahim Umar Ya Rasu
Da yake miƙa injinan, Alh. Hassan Baita, wanda shi ne shugaban taron sada zumunci na ‘yan ajin shekarar 2015 kuma wanda ya ɗauki nauyan sayan injinan ya ce, wannan somun-taɓi ne kuma lokaci bayan lokaci za a ke irin waɗannan ayyuka don bunƙasa wannan sashe.
A nasa jawabin, tsohon Sakataren Ƙungiyar Hausa ta Jami’ar Bayero, Muhammad Bashir Amin, ya bayyana ƙudurinsu na bunƙasa sashen ta hanyar bijiro da ayyukan da za su ciyar da sashen gaba, ya kuma buƙaci malamai da su ƙara kyautata alaƙarsu da ɗalibansu su ja su a jika, su ɗauke su tamkar ‘ya’yan da suka haifa, saboda hakan zai ƙara yi wa ɗaliban ƙaimi wajen tunawa da su bayan Allah ya ɗaukaka su a rayuwa.
Shugaban Sashen, Farfesa Isah Mukhtar, ya godewa ɗaliban da suka yi wannan hoɓɓasa da abun arziƙi a lokacin da ya ke shugabantar sashen, ya kuma bayyana cewa haƙiƙa irin wannan tallafi zai taimaka musu su tsallake tantancewar hukumar kula da Jami’o’i ta ƙasa da za ta yi wa sashen a shekara mai zuwa, wanda gaza samar da kayan koyo da koyarwa da kayan gudanar da aiki ka iya kaiwa ga samun babbar matsalar da zata iya kaiwa ga rufe sashen baki ɗaya.
Taron ya samu halartar mataimakin shugaban tsangayar fasaha da nazarin addinin musulunci da malaman sashen yayin bikin miƙa injinan.
Mahalarta taron daga ɓangaren malamai da ɗalibai sun jinjinawa ƙoƙarin tsofaffin ɗaliban na samar da injinan, sun kuma gode musu da fatan Allah ya yalwata arziƙinsu.