Taron kungiyar gwamnonin jihohin yankin arewa maso gabashin Nijeriya da ya gudana a Yola fadar jihar Adamawa, sun cimma matsayar samar da wutar lantarki mai karfin MW60 ko samar da wutar sola MW50, a kowace jiha cikin jihohin yankin 6.
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana haka lokacin da yake karanta sakamakon bayan taron na yini biyu Ranar Asabar a Yola, ya ce samar da wutar lantarkin zai magance matsalar karancin wutar da ake da ita a yankin.
- Adamawa Za Ta Karbi Bakuncin Taron Gwamnonin Arewa Maso Gabas Na 9 A Gobe
- Gwamnonin Arewa Maso Yamma Na Yunkurin Zamanantar Da Aikin Gona
Haka kuma gwamnan ya ce, taron ya yi la’akari da rashin hanyar dogo, don haka su ke kira ga gwamnatin tarayya da ta kammala aikin hanyar dogo a yankin.
Kazalika, taron ya lura da matsalar canjin yanayi da muhallin da yankin ke fuskanta inda ya ce, matsalar na daga cikin manyan matsalolin da ya tunkari yankin da taron ya amince da yin aiki tare da kungiyoyi kamar su ‘Great Green Wall’ da ‘Global Initiative of Carbon Credit’.
Taron ya yaba da yadda jihohin ke bibiyar matsayar da su ka cimma kan dokar ilimi 2022 da majalisar ilimin jihohin yankin ta yi wa gyara, ta kuma yi kira ga jihohin da su kara himma da habaka fannin ilimin.
Gwamna Mai Mala ya ci gaba da cewa, “mun lura an samu ci gaba a harkar tsaro a yankin, akwai bukatar kara samun hadin guiwa da aiki tare a tsakanin jihohin a bangaren aikin samar da tsaro, za mu kara aiki sosai da bangarorin jami’an tsaro saboda aikin tsaro aiki ne na kowa.
Kungiyar ta kuma sanar da cewa za ta gudanar da taronta na 10, a garin Bauchi a tsakanin 23 da 26 ga watan Fabrairun 2024.