Kwamitin da gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri, ya dora wa alhakin raba kayayyakin abinci da rage radadi, biyo bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi, ya bayyana tsare-tsaren ganin rabon ya kai ga mutanen da suka fi bukata.
Da yake jawabi jim kadan da kammala ganawar da mambobin kwamitin suka yi a Yola a ranar Litinin, sakataren gwamnatin jihar Awwal Bamanga Tukur, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin, ya ce za su tabbatar da gaskiya da adalci a rabon.
- Mutane Sun Daka Wa Kayan Abinci Wawa A Bayelsa Saboda Yunwa
- Tinubu Ya Umarci Rage Yawan Masu Zuwa Taron UNGA Don Rage Kashe Kudin GwamnatiÂ
Ya ci gaba da cewa “shirin zai shafi harkokin jama’a ta kowane bangare, musamman tafiye-tafiye, rage kudaden farashin kayayyakin abinci da kashi 50 bisa dari, a daukacin cibiyoyin kada kuri’a 266, a fadin jihar.
“Shirin zai kawo saukin tafiye-tafiye ga ma’aikata, ‘yan makaranta, masu kananan karfi da matafiya da ke shigowar jiha, kan haka mun samar da motocin bas-bas 10 daga kamfanin Innoson a kan kudi naira biliyan 1.06”.
Tukur, ya ce manufar shirin shi ne kawo sauki ga wahalhalun da jama’a ke ciki, ya ce “mutane mabukata kamar; matan da mazajensu suka mutu, matan da aurensu ya mutu, nakasassun mutane, makarantun kwana da kungiyoyin mata da matasa su za su amfana da shirin, za mu tabbatar kowa ya amfani” in ji Bamanga.
Haka kuma sakataren gwamnatin jihar Awwal Tukur, ya ce gwamnatin jihar ta karbi tallafin naira miliyan dubu biyu, daga gwamnatin tarayya, kari kan tirelan biyar na shinkafa, yabce ita ma gwamnatin jihar ta samar da tirela 50, na shinkafa da masara.
“Bisa umarni, za mu tabbatar da jama’a sun samu sauki, za mu tabbatar farashinmu ya karya farashin abinci a kasuwa, za mu sayarda karamin buhu a kan kudi naira dubu 10, ba kamar yadda yake a kasuwa dubu 20 ba” in ji Bamanga.
Shugaban kwamitin ya ce kwamitin yana da masu sa ido game yadda shirin zai ci gaba da gudana, ya roke ‘yan jaridu da su rika bibiyan aikin kwamitn, ana dai tsamammin za a fara aikin a ranar Laraba.