Gwamnatin tarayya, a ranar Talata, ta tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa za ta yi amfani da fasaha wajen inganta samar da abinci a wani mataki na kokarin da take yi na bunkasa tattalin arziki ta bangaren amfani da harkokin noma.
Babban Sakataren ma’aikatar noma da wadatar da kasa da abinci, Dakta Ernest Umakhihe, shi ne ya bayar da wannan tabbacin a lokacin bude taron fasahar sadarwa domin cigaba (ICT4D) domin sanya ido da bibiyar ayyukan FGN/IFAD Nigeria da ya gudana a Abuja.
- A 2024 Ne Manoma Za Su Fara Shuka Sabon Irin Masara Na ‘TELA Maize’ —Farfesa Adamu
- Yawan ‘Yan Nijeriya Ya Doshi Miliyan 223 – Shugaban NPC
Umakhihe wanda ya samu wakilcin daraktan tsare-tsare na ma’aikatar, Malam Ibrahim Tanimu, ya ce, horaswar ICT4D na da matukar muhimmanci wajen cimma manufar tsarin shugaban kasa Bola Tinubu na farfado da fata da tsammani ta hanyar farfado da bangaren harkokin noma.
Ya ce, muddin aka rungumi fasaha, to tabbas za a samu nasarar bunkasa sashin noma, don haka ya ce, Nijeriya za ta iya cimma burinta na wadatar da kasar da abinci yadda ake so.
Da yake ganawa da ‘yan jarida a gefen taron, daraktan asusun bunkasa harkokin noma ta kasa da kasa a Nijeriya (IFAD), Dede Ekoue, ta nuna gayar muhimmancin da horaswar ke da shi, inda ta ce, an shirya taron horaswar ne da manufar rungumar amfani da fasaha wajen kyautata bibiya da sa ido kan shirye-shiryen IFAD a Nijeriya.
Ta kara da cewa, hakan zai kuma bai wa manoma cikakken dama da ikon samun sabbin dabaru wajen kyautata harkokin nomansu. A cewarta, tabbas suna da yakin wannan matakin zai kawo cigaba da cigaba da inganta ayyukanta.
Kazalika, babban kwararre da shirin ICT4D Consultant, Dana Sprole, ya ce, ta hanyar horon, suna fatan cewa za a samu ilmantar da juna muhimman abubuwan da suka shafi harkokin fasahar sadarwar zamani (ICT) kuma hadin guiwar zai fa saukaka da taimaka wa manoma matuka gaya.