Wanda ya lashe zaben takarar Sanatan Kano ta tsakiya karkashin jam’iyyar APC, Alhaji Abdussalam Abdulkarim Zaura ya bayyana cewa sun daura damarar yakin cinye zabe a Kano ta tsakiya.
Ya bayyana hakan ne a cikin jawabin da ya yi a dakin wasa na Sani Abacha bayan bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.
Ya kara da cewa shi da ‘yan takarar majalisu na jiha dana tarayya da shugabanin mulki da na jam’iyya na kananan hukumomi za su zauna su fidda yadda za su yi su fatattaka Kano ta tsakiya wajen cin zabe a shekara ta 2023 da yardar Allah.
Zaura ya ce, yana tabbatarwa sa al’ummar Kano ta tsakiya cewa yanzu ne za su sami kyakkyawan wakilci da ikon Allah.
Shima Hon. Dahiru Ahmad Mai Wuddadu, mai magana da yawun Abdussalam Abdulkarim Zaura ya ce, zaben an gudanar dashi kowa ya zabi abinda yake so cikin tsari na zaman lafiya da kwanciyar hankali ba tare da an tursasa ko tilastawa kowa ba.
Ya ce, sannan kowa an bashi ‘yancinsa na damakwaradiyya ya zabi abinda ya zame masa daidai kuma cikin ikon Allah Alhaji A. A. Zaura ya sami nasara.
Hon. Dahiru Ahmad Mai Wuddadu ya yi fatan za a fito a dukkannin zabe dan aga jam’iyyar APC ta sami gagarumar nasara dan kafa Gwamnati a kowane mataki dan tabbatar da cigaban al’umma a wannan kasa.