Zaben ‘yan majalisun kasa da suka hada dana Dattawa da Wakilai an gabatar da shi ne tare da na Shugaban kasa wanda aka yi shi ranar Asabar ta makon daya gabata a duk fadin tarayyar Nijeriya.Ko shakka babu sakamkon zaben ya bada mamaki ga wadansu ‘yan majalisun da suka tsaya takara da maida majalisun biyu tamkar gidajensu na gado.
Hausawa dama sun ce ta faru ta kare an yi wa mai zane daya sata, wasu har ya zuwa wannan lokaci da ake ciki suna cikin yanayi na mamaki da kuma kamar dimaucewa,domin kuwa wasu daga cikinsu basu taba tsammanin irin wannan rana zata iya riskarsu ba, ba tare da sun yi shirin barin inda suke ba.
Ita dama rayuwa haka take kasancewa saboda, kuwa shi mutum ya san ‘ko ba dade ko ba jima watarana ba wataran bace.Al’amarin duniya dama fararrene kuma kararrene saboda dai ko ba komai mutum ya san yadda ya tashi ya ga yadda yake a gidansu,tun yana cikin abinda aka sa aka rufe masa jiki bayan an haife shi, tun bai iya komai ba,har ga shi shine Allah ya kai shi wani wurin da bai taba ko ma mafarkin zai iya zuwa can ba.
Duniyar ma da daya- daya ne aka zota hakanan kuma za’ a barta kowa ya komawa wanda ya halicce shi, saboda ai ya san ba shine ya halicci kan shi ba Allah Subhanu Wata’ala ne ya amince har ma ya samu kanshi cikin daular da yake ganin kamar ya dauwama ke nan cikinta har Abadan Abadan.Rayuwa hakika ba tada tabbas komai yana iya faruwa kowane lokaci al’amarin haka ne duk wani al’amarin da yake, to ya kwana da sanin cewa watarana ko ya shirya ko bai shirya, haka abin zai zo ma shi.
Hausawa sun ce in ana dara fidda Uwa ake yi shi yasa aka fara da Jihar Nasarawa Jiha ce ta Shugaban jam’iyyar APC na kasa Sanata Abdullahi Adamu wanda ya wakilci mazabar majalisar Dattawa ta Nasarawa ta yamma, shi tun a mazabar shi ta unguwar GRA ta garin Keffi jam’iyyar Labour Party ta kjada shi.Bugu da kari kuma jam’iyyar SDP ta lashe kujeru biyu daga cikin uku na Dattawa da suka hada da Ahmed Aliyu daya taba zama dan majalisar wakilai ta tarayya a zamanin mulkin tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo. Zai wakilci mazabar majalisar Dattawa ta Nasarawa ta yamma.Sanata Godiya Akwashiki Nasarawa ta Arewa daga nan sai Onawo Mohammed Ogoshi na jam’iyyar PDP.Akwai dan majalisar wakilai ta tarayya da zai wakilci mazabar Keffi Karu da Kokona Gaza Jonathan daga jam’iyyar SDP, wani babban koma baya ga shi Shugaban APC shine yadda jam’iyyar LP ce ta lashe zaben Shugaban kasa.Abin ya wuce ma al’amarin majalisun kasa.
Sanata Philip Tanimu Aduda da ke wakiltar Babban birin tarayya ya kwashe shekara da shekara ya na damawa a harkar siyasar Babban Birnin Tarayya Abuja, ya shafe shekara takwas yana dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Tarayya ta kananan hukumomin Abuja da Bwari.Sai dan majalisar dattawa mai wakiltar Babban Birnin Tarayya inda shi ma sauran watanni uku ya cika shekara takwas, zaben ‘yan majalisar Dattawa da aka gabatar ranar Asabar ta makon daya gabata ne ya fafata tsakanin shi da wasu ‘yan takara biyu da suka hada da Ireti Kingibe’yar-takarar jam’iyyar LP.Ta kwashe shekaru da suka kai ashirin da uku tana gwagwarmayar siyasa inda ta fito takara Sanata karkashin jam’iyyu daban- daban, sai wannan zaben shekarar 2023 ne Allah ya bata sa’a.
Dantakarar majalisar dattawa a karkashin jam’iyyar Labour Party Mista Donatus Mathew shine wanda hukumar zabe ta bayyana ya lashe zaben kujerar majalisar Wakilai ta tarayya na mazabar Kaura ta tarayya.Kafin dai haka sai yayi sana’ar Okada, ya taba yin Kansila lokacin mulkin Makarfi amma daga baya sai al’amura suka canza ma shi. Bello Nasiru El Rufai ya samu Nasarar lashe zaben dan majalisar ta wakilai ta tarayya indazai wakilci mazabar Kaduna ta Arewa. Shi ma Sadik Ango Abdullahi wanda yana daga cikin wadanda yana daga cikin wadanda maharan Jirgin kasa mai zuwa Kaduna daga Abuja, ya lashe zaben majalisar wakilai ta Tarayya ta SabonGarin Zariya.
Sanata Bala Ibn Na Allah kafin ya zama Sanata ya fara zama dan majalisar wakilai ne ta Tarayya daga shekarar daga shekara ta 2003 zuwa 2011,sai majalisar Dattawa ta kasa daga 2015 zuwa 2023,wanda bayan an kamamla zaben ne Garba Musa Maidoki na jam’iyyar PDP wanda kuma wannan shine karon shi na farko daya fara fito takara ya kuma samu damar kada wanda ya dade yana damawa a harkokin siyasar.Sanata Bala Ibn Na Allah ajin shi daya da Sanata Philip Aduda ganin yadda suka kwashe shekaru maso yawa tsakanin majalisun Wakilai da Dattawa na kasa.
Jihar Gombe ma akwai Sanata Ibrahim Gombe ta tsakiya Dankwambo wanda tsohon gwaman Jihar Gombe ne, a shekarun da suka gabata yayi kokarin tsayawar Sanata amma abin yaci tura sai wannan lokacine.Kamar dai an yi ma shi ritaya ne ko yayi ma kanshi duk da yake dai duk al’amarin na Allah ne duk lokacin daya ba mutum lokacin ne yaga yafi dace da shi.Akwai kuma Sanata Anthony Siyako Gombe ta Arewa.
Jihar Kano kuma akwai guguwar siyasar Kwankwansiyya ta jam’iyyar NNPP wadda tayi awon gaba ta wasu shahararrun ‘yan siyasar ta Kano biyu da suka hada da Sanata Kabir Gaya mai wakiltar mazabar Kano ta Kudu da suaka hada da Sanata Kabiru Ibrahim Gaya an zabe a majalisar Dattawa ne sau uku a zabubbukan shekara ta 2007, 2011, 2015 da kuam 2019. Shi ma dan gida ne idana ana maganar majalisar kasa sai kuma a zaben shekara ta 2023 inda bai samu nasara ba lashewa ba, bayan Kawu Sumaila na jam’iyyar NNPP ya kada shi a zaben,saboda ko karamar hukumar shi ta Gaya bai ci ba.
Jihar Katsina Sanata Ahmed Babba Kaita wanda ya koma jam’iyyar PDP daga APC bai samu nasara ba saboda Alhaji Nasiru Sani Zangon Daura dan takara majalisar Dattawa na jam’iyyar APC na Katsina ta Arewa shine ya kada shi.Abdul’aziz Musa ‘Yar’aduwa kanine na tsohonShugaban kasa marigayi Umaru ‘Yar’aduwa shi ya lashen zaben mazabar majalisar Dattawa ta Katsina ta tsakiya. Sanata Ahmed Babba Kaita shi ma ya dade a majalisar kasa domin ya shafe shekaru a tsakanin majalisar Wakilai da majalisarDattawa ta kasa,amma a wannan zaben 2023 sai Allah ya ba wani. Muntari Dandutse an zabe shi a matsayin sabon Sanata mai wakiltar mazabar Katsina ta Kudu tsohon dan majalisar wakilai neta tarayya wanda har yanzu bai kai ga kammala wa’adin shi ba.
Zabar sabbin ‘yan majalisar Dattawa da wakilai na kasa a ranar 25 ga watan Fabrairu 2023 wata dama ce da suma zasu bada tasu gudunmawa wajen cigaban kasa,maimakon yadda wasu ke mamayeb ta su maida wurin kamar wani gidansu na gado.Wani sauyi ne daya zo daga Allah inda ya bada wata dama har aka kai ga zaben su sabbin ‘yan majalisun na kasa.Akwai wadanda wadansu gwamnonin da ke kammala wa’adinsu watanni uku masu zuwa, sun tsaya takara amma Allah bai yadda ba hakar tasu bata cimma ruwa ba,don haka yadda Allah ya so aka dama ta hakane za’a sha ta.