Hukumar Yaki Da Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC), ta cafke takardar kudi Naira miliyan N32,400, 000.00 da ake zargin an ware su ne domin sayen kuri’un jama’a a jihar Legas.
Kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce, jami’ansu da ke aiki shiyyar Legas ne suka samu nasarar cafke kudin ranar Juma’a.
- Matsayin Alkaluman Kirkire-Kirkiren Sin Ya Daga Zuwa Na 11 A Duniya
- MOC:Galibin Manyan Kamfanonin Kasa Da Kasa Suna Son Neman Bunkasuwa A Kasar Sin Cikin Dogon Lokaci
Uwujaren ya kara da fada a cikin wata sanarwa cewa an cafke wani da zargi tare da kudin (amma ba su bayyana sunansa ba) kuma a cewarsa yanzu haka yana fuskantar tambayoyi a ofishin EFCC.
A cewarsa, “A kokarin hukumar mu na dakile sayen kuri’u a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da da zai gudana a gobe, mun samu nasarar cafke kudi har naira N32,400,000 da ake zargin sayen kuri’u za a yi da su a Legas.
“An tafi da wanda ake zargi da kudin domin fadada bincike da masa tambayoyi.”
“Shugaban hukumar, Abdulrasheed Bawa ya jibge jami’ansa da za su sanya ido a yayin zaben kuma an umarcesu da kada su bayar da kofa ga kowace na yin sayen kuri’u.”