Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta dage zamanta na tattara sakamakon zabe daga jihohi zuwa gobe Litinin 27 ga Fabrairu, 2023 da misalin karfe 11 na safe.
Ku tuna cewa, Cibiyar tattara sakamakon an bude ta a hukumance ne da misalin karfe 1 na ranar Lahadi sannan aka tafi hutu zuwa karfe 6 na yamma bayan an zauna kasa da mintuna 30 sabida babu wani sakamakon zaben shugaban kasa daga jihohi 36 na tarayya da babban birnin tarayya Abuja.
Shugaban zabe, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ci gaba da zama da misalin karfe 6 na yammacin ranar Lahadi, ya kira jami’in zabe na jihar Ekiti, Farfesa Akeem Lasisi, wanda ya shirya don gabatar da sakamakon zabe kamar haka:
Farfesa Lasisi ya gabatar da sakamakon kamar haka:
APC – 201,494
LP – 11,397
NNPP – 264
PDP – 89,554
Yawan kuri’un da aka kada – 314,472