Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, ya ce zaben 2023 ya kasance mafi inganci zabe da aka taba gudanarwa a tarihin Nijeriya.
Shugaban majalisar, ya lura ce an samu ci gaba a kokarin kasar nan na tabbatar da sahihin zabe.
- 2023: Jihohin Da INEC Ta Bayyana Sakamakon Zaben Gwamnoni
- Magoya Bayan Peter Obi Sun Gudanar Da Zanga-Zanga A Abuja Kan Zaben 2023
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban majalisar ya tabbatar da cewa majalisar za ta tabbatar da amincewa da kudirin dokar hukumar laifuffukan zabe kafin karewar wa’adinta a watan Yuni.
Gbajabiamila ya bayyana haka ne a ranar Talata a Abuja yayin da yake maraba da takwarorinsa da suka dawo daga zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha da aka kammala.
“Mun tabbatar an samu ci gaban da aka samu a kokarin da muke yi na tabbatar da zaben da za mu yi alfahari da shi,” in ji shi.
A cewar Gbajabiamila, gyaran dokar zabe da majalisar dokokin kasar nan ta 9 ta yi, ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta harkokin zabe ta hanyar amfani da na’urorin fasaha don saukaka tantance masu kada kuri’a da yada sakamakon zabe.
“A kowace sabuwar kakar zabe, muna kara fahimtar bangarorin da ke bukatar sauye-sauye don tabbatar da samun kyakkyawan sakamako a lokaci na gaba. Dole ne a ci gaba da gudanar da gyare-gyaren da ya dace. A matsayin matakin farko da ya dace, ya kamata Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta hada kai tare da masu ruwa da tsaki don samar da sahihiyar hanyar tantance tsarin zaben. Wannan ya zama dole don sanar da karin gyare-gyare da ingantawa,” in ji shi.
A halin da ake ciki kuma, Gbajabiamila ya lura cewa kudurorin gyara kundin tsarin mulkin kasar nan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu a makon jiya za su ciyar da tarayyar Nijeriya gaba tare da kusantar da kasar wajen cimma burinta na kasa baki daya.
“Lokacin da muka fara aikin duba kundin tsarin mulki a majalisar wakilai ta 9, na ce wannan wata dama ce ta samar da kundin tsarin mulki wanda zai warware matsaloli da dama da ke damun al’ummarmu da kuma kawo mana cikas.
“A makon da ya gabata, Mai Girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu kan gyare-gyaren kundin tsarin mulkin kasar nan da majalisar dokoki ta kafa da kuma majalisun jihohin kasar nan suka amince da su.
“Wadannan gyare-gyaren tsarin mulkin sun hada da gyare-gyaren da za a iya dauka don kira da kuma yadda ake gudanar da harkokin mulkin Nijeriya, musamman game da batun raba madafun iko ga jihohi da karfafa shari’a da majalisa a matakin kasa,” in ji shi.