• English
  • Business News
Thursday, October 30, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zaben Fidda-Gwanin APC: A. A Jinjiri Ya Maka Bashir Machina Kotu

by Muhammad Maitela
3 years ago
Machina

Ga dukan alamu zaben fidda-gwani da jam’iyyar APC na Sanatan Arewacin Yobe ya bar baya da kura, wanda ya jawo a ranar Juma’a daya daga cikin ‘yan takarar, Abubakar Abubakar Jinjiri, ke kalubalantar nasarar da Bashir Sheriff Machina ya samu zuwa kotu.

Hon. Machina wanda ya lashe zaben da kuri’u 289 a zaben, wanda kuma yake sa-toka sa-katsi tsakanin sa da shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Ahmed Ibrahim Lawan.

  • Ya Yi Yunkurin Arcewa Bayan Daba Wa Mai Ciki Wuka Ta Mutu
  • Kotun Daukaka Kara Ta Yi Watsi Da Karar Buhari Kan Sashe Na 84(12) Na Dokar Zabe

Haka zalika, bayan da Lawan ya sha kasa a zaben fidda-gwani na shugaban kasa da APC ta gudanar, ya gamu da turjiyar Machina bisa kin janye masa ya ci gaba da jan zarensa a kan kujerar Sanatan Arewacin Yobe, duk da goyon bayan da yake samu daga uwar jam’iyyar APC ta kasa.

A. A Jinjiri yana daga cikin jerin ‘yan takarar da suka mika sunayensu domin kalubalantar zaben fidda-gwani a jihar Yobe, a gaban mai shari’a Fadima Murtala Aminu ta Babbar Kotun Tarayya, da ke Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

Da yake zanta wa da manema labarai a gaban kotun, lauyan mai kara, Barists Usman Lukman Nuhu, ya bayyana cewa wanda yake wakilta ya na kalubalantar Machina, tare da uwar jam’iyyar APC ta kasa da ta jihat Yobe, hadi da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), bisa rashin sanya sunan shi a cikin yan takara.

LABARAI MASU NASABA

An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato

APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba

Ya kara da cewa, an hana Jinjiri ya shiga zaben fidda-gwani na Sanatan Arewacin Yobe, duk da kuwa yadda ya halarci wajen da aka gudanar da shi.

“Kuma na yi imani cewa kuna da kofi na takardar sakamakon zaben fidda-gwanin, wanda da kanku na san kun tabbatar babu sunan wanda nake bai wa kariya a takardar sakamakon zaben. ” in ji shi.

Har wa yau, ya ce kin saka sunan dan takara abu ne wanda ya saba wa dokar kundin tsarin mulki ta sashe na (84) da karamin sashe na (3 da 4) na dokokin zabe.

Bugu da kari, akwai kararrakin zaben fidda-gwani guda bakwai wadanda ke kalubalantar sakamakon zaben fidda-gwanin da jam’iyyar APC da ta gudanar.

Haka kuma, mai shari’ar ta ayyana ranar 21 ga watan July 21, 2022 a matsayin lokacin fara shari’ar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato
Manyan Labarai

An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato

October 28, 2025
Machina
Manyan Labarai

APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba

October 27, 2025
Jam’iyyar NNPP A Kaduna Ta Ƙaryata Batun Tsige Shugabanta
Siyasa

Jam’iyyar NNPP A Kaduna Ta Ƙaryata Batun Tsige Shugabanta

October 24, 2025
Next Post
APP Za Ta Maka Tinubu A Kotu Kan Rashin Takardun Makaranta

APP Za Ta Maka Tinubu A Kotu Kan Rashin Takardun Makaranta

LABARAI MASU NASABA

Sakamakon Nazarin CGTN Ya Yabawa Gudunmuwar Sin Ga Dunkulewar Yankin Asiya Da Pasifik

Sakamakon Nazarin CGTN Ya Yabawa Gudunmuwar Sin Ga Dunkulewar Yankin Asiya Da Pasifik

October 29, 2025
Asuu

Gwamnatin Tarayya Ta Saki Naira Biliyan 2.3 Ga ASUU

October 29, 2025
Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki

Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki

October 29, 2025
Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

October 29, 2025
An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

October 29, 2025
majalisar kasa

Majalisar Wakilai Ta Amince Da Bukatar Amso Bashin Dala Biliyan 2.34 A Kasuwar Jari Ta Duniya

October 29, 2025
An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

October 29, 2025
Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC

Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC

October 29, 2025
Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a

Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a

October 29, 2025
COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa 

COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa 

October 29, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.