Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta gargadi jam’iyyun siyasa da magoya bayansu gabanin shiga zaben gwamnoni da za a yi ranar Asabar.
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya yi wannan gargadin a ranar Talata a Abuja yayin wani kwamitin tuntubar hukumomin tsaro kan harkokin zabe.
- ‘Yan Takaran Gwamna 8 Sun Mara Wa Gwamnan Gombe Baya
- Dan Takarar Gwamnan PDP A Delta Ya Tsallake Rijiya Da Baya Daga Harin ‘Yan Bindiga
Yayin da ake sa ran gudanar da zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha da za a yi ranar Asabar, INEC ta gargadi jam’iyyun siyasa da magoya bayansu da kada su shiga duk wani tashin hankali da zai iya kawo cikas ga zaben.
Ya kuma yi kira ga jam’iyyun siyasa da su dauki kansu a matsayin masu ruwa da tsaki a zabe mai zuwa ta yadda za su tunkari shi a matsayin takara ba yaki ba.
Shugaban na INEC ya kara da cewa an yi wa jami’an tsaro bayanai dalla-dalla kan yadda zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da suka hada da wuraren da aka gudanar da rumfunan zabe da wuraren tattara sakamakon zabe tare da bayyana kwarin gwiwar cewa za su yi aikinsu da kwarewa kamar yadda aka saba a baya.
“Saboda haka, muna sa ran shirin tura sojoji tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro, leken asiri.
“A jiya ne hukumar ta gudanar da wani taron tattaunawa da dukkan kwamishinonin zabe, inda muka duba shirye-shiryen zaben. Baya ga fasahar zabe, kayan aiki da sauran batutuwa da dama, an kuma tattauna batun tsaro,” in ji Yakubu.
Shugaban INEC ya kara da cewa hukumar a shirye take ta tunkari duk wasu shari’o’in da suka shafi laifukan zabe, ya kuma yabawa sufeto-janar na ‘yansanda bisa umarnin da ya bayar a baya-bayan nan cewa, har yanzu irin wadannan shari’o’in na hannun ‘yansanda.
“Ya kamata su guji tashe-tashen hankula da za su iya kawo cikas ga zaben ko kuma kawo cikas ga tsaron ma’aikatanmu, masu sa ido, kafafen yada labarai,” in ji shi.
“Hukumar ta samu kwarin gwiwa bisa umarnin da babban sufeton ‘yansanda ya bai wa jihohi.
“Muna sa ran karbar kararrakin da aka shigar. Nan take za mu kafa wata tawaga ta lauyoyi da za ta tunkari irin wadannan shari’o’i.”