- Yadda Zaben Shugaban Kasa Ya Canza Lissafi
- Za Mu Gyara Kura-kuranmu A Zaben Gwamna – INEC
Bayan kammala zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasa, alamu sun nuna cewa akwai fafatawa mai zafi a wasu jihohin duba da yadda sakamakon zaben shugaban kasa ya kaya.
Wasu gwamnoni sun kasa yin nasara a jihohinsu a lokacin zaben shugaban kasa, wanda hakan ta janyo musu babban kalubale wajen kokarin sun samu nasara a zaben gwamna.
Bincike ya nuna cewa a Jihar Legas da jam’iyyar APC ta sha kaye a hannun jam’iyyar LP a zaben shugaban kasa, Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya yi ta ganawa da kungiyoyi daban-daban da shugabannin al’umma domin neman goyon bayansu don sake zabensa.
Hakazalika, a Jihar Oyo da APC ta doke PDP mai mulki, Gwamna Seyi Makinde da magoya bayansa sun sake yin wani sabon yunkuri na ganin sun kai ga nasara a zaben gwamna.
A halin da ake ciki dai wasu gwamnoni masu barin gado da suka sha kaye a jihohinsu a zaben shugaban kasa, amma kuma suke da burin dora amintattun mukarrabansu kan karagar mulki, suma sun fara fargabar yiwuwar rasa jihohinsu.
Jihohin sun hada da Benuwai, Abiya, Kuros Riba, Inugu, Delta, Kano, Kaduna, Filato, Katsina da Gombe.
A zaben shugaban kasa, Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir el-Rufai, wanda yana daya daga cikin masu rike da madafun iko a jam’iyyar APC mai mulki, ya sha kaye a jiharsa a hannun jam’iyyar PDP, inda a halin yanzu makomar wanda yake so ya zama magajinsa, Uba Sani take tangal-tangal ganin yadda jam’iyyar PDP ta wawushe kujerun majalisa a jihar.
Domin kar jihar ta fada a hannun jam’iyyar adawa, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi kira ga al’ummar Kaduna da su zabi Uba Sani, wanda ya bayyana shi a matsayin mai kwazo da jajircewa.
A halin da ake ciki, jam’iyyar APC reshen Jihar Legas ta bayyana kwarin gwiwar cewa Sanwo-Olu zai yi nasara a zaben gwamnan da za a yi ranar Asabar.
Kakakin jam’iyyar a jihar, Mista Seye Oladejo ne ya bayyana hakan a wata hira ta wayar tarho da Sunday PUNCH ta yi da shi, inda ya bayyana nasarar da jam’iyyar LP ta samu a zaben shugaban kasa a matsayin bazata.
Sai dai jam’iyyar LP a jihar ta bayyana kwarin gwiwar cewa dan takararta, Gbadebo Rhodes-Bibour, zai lashe zaben gwamna.
Da yake magana a wata hira da Sunday PUNCH, kakakin LP a jihar, Olubunmi Odesanya, ya ce, “Muna da kwarin gwiwa dan takararmu yana da damar lashe zabe kuma muna da kwarin gwiwa a matsayinmu na jam’iyyar LP.
A Jihar Ebonyi kuwa gabanin zaben shugaban kasa, gwamna Dabe Umahi ya bayyana cewa ya kulle Jihar Ebonyi ga dan takarar shugaban kasa na APC, Tinubu, sai dai ya yi rashin nasara ga jam’iyyar LP.
Jam’iyyun PDP da LP, a ranar Asabar, sun bayyana kwarin gwiwar cewa za su samu gagarumar nasara a siyasance a zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokoki a jihar.
Manyan ‘yan takarar kujerar gwamna a jihar sun hada da Francis Nwifuru na APC, Cif Ifeanyi Odii na PDP da Edward Nkwegu na LP.
A Jihar Inugu kuwa, jam’iyya PDP ta rasa ‘yan majalisar wakilai guda bakwai a wurin jam’iyyar LP, yayin da gwamna Ifeanyi Ugwuanyi ya kasa samun kujerar sanata na yankin Inugu ta arewa wanda Cif Okey Ezea na jam’iyyar LP ya samu nasara.
Har yanzu dai ana ci gaba da fafatawa a zaben sanata a yankin Inugu ta Yamma duk da cewa INEC ta bayyana dan takarar jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben, yayin da za a sake gudanar da sabon zabe na sanata a yankin Inugu ta gabas a ranar Asabar bayan kashe dan takarar jam’iyyar LP, Cif Oyibo Chukuwu.
Manyan ‘yan takarar kujerar gwamnan sun hada da Uche Nnaji na APC, Peter Mbah na PDP da Chijioke Edeoga na LP.
A Jihar Kano a zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya, jam’iyyar NNPP ta amsa jihar da karfin tuwo, a yayin da dan takararta na shugaban kasa, Rabi’u Kwankwaso ya samu gagarumar nasara a Jihar Kano, sannan kuma jam’iyyar ta lashe kujerun sanatoci uku da mafi yawan kujerun majalisar wakilai.
Domin ganin sun samu nasara a zaben gwamna, gwamna da mukarrabansa da kuma jami’an jam’iyyar APC sun shiga tattaunawar sirri na janyo hankulan masu kada kuri’a a zaben na ranar Asabar.
Akwai dai babban kalubale ga jam’iyyar APC a Jihar Kano daga wurin jam’iyyar NNPP ganin yadda ta samu nasara.
Hakazalika, a Jihar Katsina ba kamar yadda ake tsammani ba, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kasa samun nasara ga dan takarar jam’iyyarsa a jiharsa, yayin da PDP ta doke APC.
Sai dai jam’iyyar APC ta lashe kujeru uku na ‘yan majalisar dattawa da kuma tara daga cikin kujeru 15 na majalisar wakilai a jihar. Jam’iyyar PDP ta lashe sauran kujerun majalisar wakilai shida.
Fafatawar da za ta fi zafe ne don maye gurbin Gwamna Aminu Masari, za a fafata ne da dan takarar jam’iyyar APC, Dakta Umar Dikko Radda, da dan takarar jam’iyyar PDP, Sanata Lado Yakubu Darmake, da Nura Khalil na NNPP, Imrana Jino na jam’iyyar PRP da Ibrahim Zakkari na jam’iyyar SDP.
Sai dai a Jihar Kaduna masu zabe za su tantance wanda zai gaji Gwamna Nasir el-Rufai a tsakanin dan takarar APC, Uba Sani, Isa Ashiru na PDP, da Jonathan Asake na LP.
Jam’iyyar PDP ta lashe zaben shugaban kasa da kujerun sanatoci uku a jihar, inda ta samu nasara a zaben ‘yan majalisar wakilai da kujeru 10 cikin 16.
Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Zai Iya Tasiri A Kan Wasu Jihohi
Sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasa da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata na ci gaba da tada kura a harkokin siyasar kasar nan. A karon farko tun 1979, ‘yan takarar shugaban kasa uku sun yi takara da wuya. A ranar Larabar da ta gabata ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta ayyana Asiwaju Bola Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin zababben shugaban kasa. Ya yi nasara ne cikin mawuyacin hali.
Tinubu ya samu kuri’u 8,794,726, inda ya doke babban abokin hamayyarsa, Alhaji Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 6,984,520. Tinubu da Atiku kowanansu ya lashe jihohi 12.
Dan takarar jam’iyyar LP, Mista Peter Obi, ya samu kuri’u 6,101,533, inda ya zo na uku, kuma ya kuma lashe jihohi 11 da Babban Birnin Tarayya.
Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya zo na hudu da kuri’u 1,496,687, ya kuma lashe jiharsa ta Kano.
Tinubu ya lashe jihohin Ekiti, Kwara, Ondo, Oyo, Ogun, Jigawa, Nija, Benuwai, Kogi, Borno, Zamfara da Ribas.
Atiku ya yi nasara a jihohin Osun, Yobe, Gombe, Adamawa, Katsina, Akwa Ibom, Bauchi, Bayelsa, Kaduna, Kebbi da Sakkwato.
Obi ya samu rinjaye a Abiya, Anambra, Ebonyi, Imo, Delta, Kuros Riba, Legas, Edo, Inugu, Plateau, Nasarawa da Babban Birnin Tarayya wato Abuja.
Yadda Zaben Shugaban Kasa Ya Canza Lissafin
Duk da cewa Atiku da Obi sun yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasar, wadanda suka sha alwashin neman hakkinsu a kotu kuma tuni suka fara yin hakan, zaben ya sauya salon siyasar Nijeriya ba kamar yadda aka saba ba.
Mafi yawancin manyan ‘yan siyasa siyasa sun sha kashi a rumfunan zabe. Kusan gwamnoni 20 ne ba su iya kai bantansu a jihohinsu ba a zaben shugaban kasa. Da yawa daga cikinsu sun yi rashin nasara a yunkurinsu na zuwa majalisar dattawa. Sanatoci da ’yan majalisar wakilai da dama sun sha kaye a wannan zabe.
A karon farko tun 1999, sabuwar majalisar dokokin kasar za ta samu wakilai daga jam’iyyu guda takwas. A majalisar dattawa ta 10, za a samu jam’iyyu bakwai, yayin da majalisar wakilai ta 10 za ta kasance da jam’iyyu takwas.
A halin yanzu, daga cikin kujeru 325 na APC, daga cikin kujerun majalisar wakilai 360 an karbi kujeru 162. PDP na da 102, LP 34, NNPP 18, SDP 2 da YPP na da 1.
A majalisar dattawa kuwa, a kujeru 98 daga cikin 109, APC na kan gaba da kujeru 57, PDP 27, LP 7, NNPP 3, SDP 2, YPP1, da APGA1.
Ana dai danganta wannan sakamako mai ban mamaki da irin yakin neman zaben da manyan ‘yan takara hudu suka yi, musamman Peter Obi da Kwakwanso. Ta hanyar jam’iyyun LP da NNPP ke cin gajiyar nasarar da suka taba samu a tarihin siyasar Nijeriya. A majalisa ta 10, LP za ta samu mambobi akalla 41, ita kuma NNPP 21. Adadin na iya karuwa idan ta samu karin kujeru 46 (majalisar wakilai 35, da majalisar dattawa 11) da za a gudanar a ranar 11 ga watan Maris.
Sakamakon Zaben shugaban Kasa Zai Iya Tasiri A Kan Wasu Jihohi
Bayan da tsunami da ya biyo bayan zaben ranar 25 ga Fabrairu, an samu tashi tsaye a cikin harkokin siyasan Nijeriya. ‘Yan siyasa sun dawo kan hayyacinsu. Da yawa daga cikin manyan ‘yan siyasa sun hau kan seti.
A ranar Asabar ne dai za a fafata a zaben gwamna a jihohi 28 da kujeru 993 na majalisar dokokin jiha.
Ba za a yi zaben gwamna a jihohin Anambra, Bayelsa, Edo, Ekiti, Ondo, Osun, Kogi da kuma Imo ba, saboda hukuncin kotun koli da ya sanya gwamnonin su gudanar da zabe a mabambantan ranaku da ya saba da ranar 29 ga watan Mayu lokacin mika mulki.
Ko da yake, gwamnonin jihohin bakwai ba sa takara, shin za su kai ‘yan takarar jam’iyyunsu a zaben majalisar? A cikin bakwai, gwamnonin Anambra da Edo sun kasa bai wa APGA da PDP nasara a zaben shugaban kasa.
A cikin jihohi 28 da za a gudanar da zaben gwamna a ranar Asabar, 10 ne ke neman sake tsayawa takara, yayin da 18 wa’adinsu ya shude.
Gwamnoni hudu daga cikin 10 (Legas, Oyo, Gombe da Nasarawa) da ke neman a sake zabensu sun gagara lashe jihohinsu a shugaban kasa.
Hakazalika, gwamnoni hudu ne kawai daga cikin 18 da wa’adinsu ya shude (Akwa Ibom, Bayelsa, Sakkwato da Jigawa) suka samu nasara ga jam’iyyunsu a zaben shugaban kasa. Duk da cewa, Nyesom Wike na jam’iyyar PDP ne, amma rahotanni sun ce ya yi wa APC aiki a zaben shugaban kasa saboda takun-saka tsakaninsa da Atiku Abubakar.
A yayin da ‘yan Nijeriya ke shirin yin zabe zagaye na biyu a 2023, sai dai hakan bai kasance ba a ranar 25 ga watan Fabrairu. A yanzu dai jam’iyyu uku ne kawai da suka hada da APC, PDP da APGA ke da gwamnoni. Shin yawan jam’iyyun da gwamnoni za su karu bayan zabe gwamnoni? Shin gwamnonin da suka kasa kai bantansu a ranar 25 ga Fabrairu za su iya kai wa a zaben gwamna? Wadanda suka ba da gudummawa za su ci gaba da cin nasara ko kuwa akasin haka?
Za Mu Gyara Kura-kuranmu A Zaben Gwamna – INEC
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sha alwashin za ta gyara kura-kuran da aka samu a lokacin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisan tarayya, a lokacin zaben gwamna da kuma ‘yan majalisan dokokin jihoji.
INEC ta bayyana cewa za ta yi amfani da na’urar BBAS wurin bayyana sakamakon zaben a ranar 11 ga watan Maris lokacin gudanar da zaben gwamna da na ‘yan majalisa jihohi.
An samu cikas da na’urar a lokacin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasar da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, lamarin da ya kai ga sukar hukumar zabe da kin amincewa da sakamakon zabe da jam’iyyun adawa suka yi.
Da yake magana a ranar Asabar a Abuja, shugaban hukumar INEC, Farfesa Yakubu Mahmood, ya ce duk da kalubalen da ake fuskanta ta BBAS, za a sake amfani da ita wajen tantance masu zabe da kuma bayyana sakamakon zabe.
Ya ce: “Tsarin BBAS ya yi nisa wajen tsaftacewa da tantance masu kada kuri’a kamar yadda ake iya gani daga sakamakon zaben da aka yi kwanan nan. Tun a makon da ya gabata, hukumar ta kara yin nazari kan fasahar don tabbatar da cewa an kauce wa kura-kuran da aka samu, musamman wajen shigar da sakamakon. Muna da tabbacin cewa ci gaba da tsarin zai yi aiki da kyau.
“Har ila yau, hukumar ta yaba da hakuri da fahimtar ‘yan Nijeriya. Ba mu dauki wannan a wasa ba. Haka nan muna godiya da shugabannin siyasa, na gargajiya, na addini da na al’umma da suka nemi a kwantar da hankula.
“Hakazalika, hukumar ta yaba da rawar da masu sa ido na kasar waje suka takawa, wadanda wasunsu har yanzu suna kasar nan. Muna kira ga irin wadannan masu saka ido kara kwazo a zaben gwamna da na ‘yan majalisun jihohi, domin suna da matukar muhimmanci a babban zaben da aka amince musu su saka ido.
“Sannan hukumar ta yaba wa duk masu sa ido na cikin gida saboda rahotannin da suka bayar wanda zai taimaka mana matuka yayin da muke kammala babban zaben 2023. Muna sa ran samun cikakkun rahotannin”.
Shugaban INEC ya kara da cewa hukumar za ta yi aiki tukuru domin shawo kan kalubalen da aka fuskanta a zaben da ya gabata.
Ya ce za a kara gudanar da horaswar ga ma’aikatan wucin-gadi saboda ayyukan hukumar su kara inganci ba tare da samun tarnaki ba.