An jibge tare da baza jami’an tsaro a garin Osogbo, babban birnin Jihar Osun, yayin da jihar ke shirye-shiryen karshe na zaben gwamna da za a gudanar a gobe Asabar.
Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), ne a yau Juma’a ya ruwaito cewa an ga ‘yan sandan Nijeriya an jibge su a muhimman wurare.
- Hon. Ali Baba Ya Bayar Da Tallafin Karatu Ga Dalibai 300 A Zariya
- Nada Kashim Mataimakin Tinubu Ya Dumama Siyasar Nijeriya
Haka zalika an ga motocin yaki, dauke da makamai na sojoji suna sintiri a cikin garin.
An kuma ga jami’an hukumar tsaron fararen hula ta Nijeriya (NSCDC) a wurare daban-daban.
Haka zalika an ga jami’an hukumar kiyaye hadura ta kasa (FRSC) a wurare masu muhimmanci da ke kula da zirga-zirgar ababen hawa a cikin garin da kuma wajensa.
Ofishin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, da ke kan titin Gbongan/Osogbo ma cike ya ke da jami’an tsaro.
Idan dai za a iya tunawa babban Sufeton ‘yan sandan Nijeriya, (IGP), Usman Alkali Baba, ya ce za a tura jami’an ‘yan sanda 21,000 domin gudanar da zaben gwamna a jihar.