Shugaban Hukumar Zabe ta kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya gargadi ma’aikatan hukumar da aka tura gudanar da aikin zaben gwamnan jihar Osun, a yau Asabar cewar su kwana da sanin cewa sun karbi rantsuwa don samun nasarar gudanar da zaben.
Jam’iyyu 15 ne za su fafata a zaben na yau, inda masu fashin baki a harkar siysar jihar suka yi hasashen cewa, zaben zai kasance ne a tsakanin APC da kuma PDP.
- ‘Yan Sanda Sun Kara Cafke Wani Fursuna Da Ya Arce Daga Gidan Yarin Kuje A Katsina
- Bayan Daukar Rafinha, Barcelona Ta Taya Lewandowski
A cikin sanarwar da Yakubu ya fitar a jiya Juma’a, ya umarci duk ma’aikatan hukumar da aka tura gudanar da zaben da su tabbatar da sun nuna kwarewarsu don a gudanar da sahihin zaben na gwamna.
A cewarsa, “‘Yan Nijeriya da kuma alummar jihar ta Osun mu za su zarga in har ba mu yi abin da ya kamata ba a yayin gudanar da zaben.
“Za su kuma lura da yadda muka tafiyar da zaben da sakamakon zaben da kuma matakan da muka dauka don gudanar da zaben.”