A kwanakin nan ne jam’iyyar PDP ta gudanar da zaben shugabannin a matakin kananan hukumomi, sai dai kuma zabe ya bar baya da kura wanda ya haifar da wani sabon rikici a cikin jam’iyyar PDP bayan zargin da ake yi wa mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa, Ambasada Illiya Damagum da sakataren gudanar da zabe, Umar Bature na sauya sakamakon zaben da aka gudanar a jihohi.
Wannan bayanin ya fito ne daga bakin tsohon sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na kasa, Kola Ologbondiyan, wanda kuma ya caccaki Damagum da sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Samuel Anyanwu, kan rubuta wa kotun daukaka kara da ke Jihar Ribas cewa jam’iyyar za ta ci gaba da daukaka kara kan ‘yan majalisar dokokin Jihar Ribas 27 da suka sauya sheka, sabanin matakin da aka dauka kan mai bai wa jam’iyyar shawara kan harkokin shari’a Mista Ajibade.
- Sin Ta Kira Taron Binciken Manufofin Gaggauta Aikin Raya Yankin Yammacin Kasar
- Kudirin Wa’adin Shekaru 6 Ga Shugaban Kasa Ya Tsallake Karatu Na Farko
Tsohon sakataren yada labaran jam’iyyar ya ce mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa ya saba wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar ne ta hanyar daukar wannan mataki ba tare da bin umarnin mai ba da shawara kan harkokin shari’a na kasa ba, wanda a cewarsa sashi na 42 (1) ya bai wa jam’iyyar damar zabar wakili kan harkokin shari’a.
Ologbondiyan ya yi kira ga sauran mambobin kwamitin ayyuka na kasa wadanda ba su goyi bayan matakin da Damagum ya dauka ba, su kira taron gaggawa na kwamitin gudanarwar domin kada kuri’ar rashin amincewa da shugaban riko na kasa da kuma sakataren jam’iyyar na kasa.
Karar mai lamba PHC/2177/CS/2024, ta ta’allaka ne kan takaddamar sauya sheka da ‘yan majalisar dokokin Jihar Ribas su 27 suka yi zuwa jam’iyyar APC a ranar 11 ga Disamba, 2023.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa a kwanakin baya ne jam’iyyar PDP ta gudanar da taronta na mazabu da na kananan hukumomi. Babban taron a wasu jihohin kamar Kogi da Binuwai, Katsina ya haifar da zazzafar muhawara a tsakanin shugabannin jam’iyyar a jihohin.
Sai dai da yake tattaunawa a gidan talabijin na Arise, yayin da yake mayar da martani kan lamarin Jihar Ribas, Ologbondiyan ya ce, “Lokacin da na fara ganin waccan wasikar, ban yarda ba, amma ba zato ba tsammani shugaban rikon jam’iyyar na kasa da kuma sakatarenmu na kasa sun rubuta wasika wanda ya saba wa sashe na 42 (1) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar, wanda ya ba da ikon zabar wakili na bangaren shari’a ga duk wani lamarin da ya shafi shari’a na kasa kan mai ba da shawara a harkokin shari’a na kasa.
“Cewa mukaddashin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Ambasada Illiya Damagum da Sanata Anyanwu za su gabatar da wata takarda zuwa kotun daukaka kara, ban yarda ba. Amma cikin sa’o’i 24 na tabbatar da hakan, wannan wani irin babban abin kunya ne?
“A wannan hali ne muka samu jam’iyyarmu. Kuma ban ma ga wani abin mamaki ba, musamman a Jihar Benuwai a jam’iyyarmu, Cif Sesgu Angba yana fitowa ya ba da labarin abubuwan da ke faruwa a kusan kowace jiha ta tarayya, inda aka yi kokarin murde zaben shugabannin a matakin kananan hukumomi, wanda ake zargin sakataren shirya taron, Bature da Damagum da Sanata Anyanwu suna aikatawa.
“Ban fahimci abin da ake nufi da manufar wannan duka ba, amma wannan abin damuwa ne. Kuma tun jiya shugabannin jam’iyyar suka yi ta kira da tattaunawa a tsakanin juna suna tambaya cewa, “Wannan shi ne karshe? Wannan ne irin shugabanci da muka tsinci kanmu a ciki?
“Na sha fada a baya cewa abun kunya ne mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa ya gurfana a gaban kwamitin gudanarwa da kwamitin zartarwa da kuma kwamitin amintattun jam’iyya kan saba wat sarin mulkin jam’iyyar PDP.
“Don haka zai gurfana a gaban kotu ne kan dukkan sassan jam’iyyar, saboda kawai yana son ya zauna a kan mukaminsa ko ta halin ya ya,” in ji shi.
A cewar Ologbondiyan, akwai shirin ruguza jam’iyyar, lamarin da ke faruwa a Jihar Ribas, wanda ya nuna cewa mukaddashin shugaban jam’iyyar yana tare da ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike.
Ologbondiyan ya kuma zargin Damagum da sauya jadawalin gudanar da zaben ba tare da izini ba, wanda ya tsawaita gudanar da taron kwamitin gudanarwa har zuwa watan Satumba.
A karshen makon da ya gabata ne, ‘yan majalisar tarayya na jam’iyyar adawa suka zargi Damagum da Anyanwu da shirya makarkashiyar dagula muradun jam’iyyar PDP a Jihar Ribas.
‘Yan majalisar karkashin jagorancin Hon. Ikenga Ugochinyere, sun ce Damagun da Anyawu sun nuna adawa da matakin da PDP ta dauka na mai ba da shawara kan harkokin shari’a na kasa na ganin an kawar da ‘yan majalisar da ke goyon bayan Wike da suka koma jam’iyyar APC tare da hana su cutar da muradun PDP da kuma yiwuwar tsige Gwamna Siminalayi Fubara a matsayin gwamnan Ribas.
Ugochinyere ya bayyana cewa, babbar kotun Jihar Ribas ta bayar da umarni a ranar 8 ga watan Yuli, 2024, inda ta hana manyan jami’an jihar yin mu’amala da ‘yan majalisar da suka sauya sheka.
Sai dai ya yi zargin Dakta J.Y. Musa, na shigar da kara kan wannan umarni, duk da adawar da mai bai wa PDP shawara kan harkokin shari’a ya nuna.
Ya ce, “Mai bai wa jam’iyyar shawara kan harkokin shari’a na kasa, wanda tsarin jam’iyyar ya ba shi ikon kare muradun jam’iyyar PDP, ya riga ya janye karar a ranar 24 ga Yuli, 2024, bisa la’akari da irin illar da zai iya yi wa jam’iyyar.
“A wani lamari mai ban mamaki da ya faru a ranar 15 ga Agusta, 2024, Damagum da Anyanwu sun aika da wasika zuwa kotun daukaka kara da ke Fatakwal, inda suka nesanta kansu da hukuncin kotu, tare da yin zagon kasa ga matakin da mai ba da shawara kan harkokin shari’a ya dauka,” in ji Ugochinyere.