Wata kotun majistire da ke jihar Ogudu ta umarci a garkame wani mutum mai suna Idris Umai wanda ya yi garkuwa tare da lalata wata budurwa.
Alkalin majistiren Misis M.O Tanimola, ta yi watsi da rokon da Umai, ya yi na a yi masa afuwa.
- Yawan Hatsi A Kasar Sin Zai Ci Gaba Da Karuwa A Bana
- Sin A shirye Take Ta Tallafawa Ci Gaban Kasar Gambia
Sai dai bayan zaman da kotun ta yi mai shari’a ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 5, ga watan Mayu.
Umai, wanda ke zaune a unguwar Ketu da ke garin Legas ana tuhumarsa da lafin yin garkuwa da lalata da wata budurwa.
Tun da farko dai, dansanda mai gabatar da kara Insifeto Donjour Perezi ya ce, Umai ya aikata laifin da ake zarginsa da shi a cikin watan Okotoba 2022 a Legas.
Perezi ya ce Umai ya dauki budurwar mai shekara 17, ya kai ta wani gida, kusa da gidansu lokacin da take dawo wa daga makaranta.
Lauyoyin wadanda suka shigar da karar su ne, Faziya Abubakar da Mohammed Motali da Abubakar Mohammed da Amina Aminu da kuma A’isha Ibrahim dukkansu daga bangaren wadanda suke kare yarinyar,”in ji shi.
Kamar yadda lauyoyin suka ce, wannan laifi ne da ya saba wa sashi na 173 da na 268 na dokar manyan laifuka ta jihar Legas ta shekarar 2015.
Sashi na 268, ya bayyana karara cewa, “Duk mutumin da yake da niyyar aure ko ya yi zina da mace domin ya sa ta aure shi, ko ya sadu da ita ba tare da amincewarta ba, hukuncinsa shi ne daurin shekara bakwai.