A daidai lokacin da Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ke shirin mika mulki ga sabuwar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, mun yi waiwaye kan nasarori da akasin hakan da gwamnatinsa ta samu.
Shugaban Buhari dai ya lashe zaben shugaban kasa ne a shekarar 2015, kana aka sake zabinsa a karo na biyu a 2019 da wa’adin mulkinsa ke karewa a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Buhari ya shafe shekara takwas a kan karagar mulki duk kuwa da cewa an samu nasarori da hakan ya yi zaki wa al’umman kasa, kuma a gefe guda an samu wasu tulin kura-kurai da hakan suka zama abun zafi ga ‘yan kasa.
Da fari dai, shugaba Buhari ya zo kan mulki ne da alkawuran muhimmai da suka kunshi cewa zai samar da bunkasar tattalin arziki, magance matsalolin tsaro, farfado da harkar noma, kiwon lafiya, yaki da cin hanci da rashawa, tabbatar da gaskiya da adalci a yayin gudanar da mulki, da dai sauran muhimman alkawuran da ya yi a lokacin da yake yakin neman zabe a 2015, yayin da kuma a 2019 ya fi maida hankali wajen neman jama’a da su zabeshi domin kara ayyukan da ya faro.
Buhari wanda ya amshi mulki daga hannun tsohon Shugaban kasa, Dakta Goodluck Ebele Jonathan a ranar 29 ga watan Mayun 2015, yayin da kasar ke tsaka da fama da matsalolin tsaro musamman na mayakan Boko Haram. Hawan Buhari kan mulki ke da wuya gwamnati ta tashi tsaye wajen ganin an shawo kan wannan babbar matsalar, a zahirin gaskiya gwamnatin Buhari ta yi kokarin dakile ‘yan Boko Haram, amma ba a kankanin lokacin da aka tsammata ba, ko da yake har yanzu dai ana jin motsin ‘yan Boko Haram jifa-jifa.
A bangaren tsaron ta yadda za a ce kash kuma, a yayin da gwamnatin Buhari ta ci galaban ‘yan Boko Haram, sai kuma ta samu akasi ta inda ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane suka yi tasiri sosai a gwamnatin na Shugaban kasa Muhammadu Buhari, lamarin da ake ganin kamar babbar gazawace a gareshi.
Shirye-shiren yaki da talauci da fatara: gwamnatin Buhari ta yi kokari matuka a bangaren yaki da talauci, domin kuwa an bijiro da shirye-shirye masu ma’ana matuka, illa iyaka za a iya cewa an samu kura-kurai wajen gudanar da wasu wadanda hakan bai rasa nasaba da rashawa ba.
A shekarar 2016, Shugaban Buhari ya kaddamar da shirin NSIP, shiri mafi girma a duk fadin Afrika da aka samar da niyyar fitar da jama’a daga cikin kangin talauci. Miliyoyin ‘yan Nijeriya ne suka amfana da shirin kai-tsaye a fadin kasar nan.
Kazalika, a kalla mutum miliyan biyu da suka kasance talakawa ne suke amfana da shirin ‘Conditional Cash Tranfer’ (CCT) da ake ba su naira dubu goma-goma. Wasu kuma mutum 355,000 sun samu naira 20 a karkashin shirin a fadin kasar nan.
A watan Janairun 2019 ne kuma shugaban kasan ya kaddamar da shirin ‘Nigeria’s Micro-Pension Scheme’ tsarin da ya taimaka wa ma’aikata da wadanda suke aiki a kungiyoyi dukka domin yaki da talauci da fatara.
Sannan ya samar da shirin taimaka wa matasa (SF) da mutum sama da 774,000 suka amfana a kananan hukumomi 774 a fadin kasar nan, sannan aka fito da wani shirin taimakawa na Korona (TCF) da miliyoyin masu kananan sana’o’i da magidanta suka amfana a matsayin rance mai sauki.
Shirin SF na rancen da aka samar ya taimaka wa kananan ‘yan kasuwa da jama’a sama da mutum miliyan 1.2.
A 2021, ya kaddamar da shirin DBN da aka raba biliyan 482 a matsayin rance ga kananan kamfanoni sama da 200,000.
Bankin masana’antu (BOI) ya raba sama da tiriliyan 1 a matsayin rance ga sama da manya da kananan masana’antu rance tun 2015. Da dai sauran shirye-shiryen da ya kawo domin yaki da fatara.
Hanyoyi: A bangaren shimfida hanyoyi kuwa, shugaban kasan ya tabuka abun a zo a gani domin kuwa an zuba biliyoyin naira wajen shimfida hanyoyi a shiyyoyi shida da ake da su a fadin kasar nan, lamarin da ya kara fito da kasar sosai. Daga cikin manyan ayyukan a zo a gani har da ginawa da gyara wasu filayen jirgin sama da na kasa daban-daban.
Sannan dukka a karkashin Shugaban Buhari an samar da gidaje dubbai da za a raba wa masu karamin karfi ta cikin shirin FHFL da wasu shirye-shirye daban-daban.
Tattalin arziki da noma: Shugaba Buhari ya taka rawa wajen sanya jama’a su yi noma da kansu da maida hankali kan albarkatun da Allah ya huwace wa kasar nan, hakan ya samu asali ne ta tsarinsa na rufe iyakoki da ake ganin ya taimaka wajen maida hankali kan kayan da ake fitarwa a cikin kasar nan.
Sakamakon hakan, manoma da dama sun farka sun kara rungumar noma da kuma kiwo, ko da yake har yanzu wasu na sukar tsarin rufe iyakokin kasa. Ko shakka babu, Buhari ya taka rawa wajen bunkasa noma.
Sadarwa:
kazalika, za a iya cewa an samu nasarori sosai a bangaren sadarwar zamani a karkashin Buhari ta hanyoyi daban-daban da kuma wayar da kan mutane kan fasahar sadarwar zamani. Ko da yake ta wani bangaren ana ganin gazawarsa da har zuwa yanzu ya kasa fito da hanyar da za ake iya bin sawun wayoyin masu garkuwa da mutane da suke kira domin neman kudin fansa.
Arzikin Mai:
A karkashin Shugaba Buhari ne aka samu damar kaddamar da matatar Mai ta kamfanin Dangote wacce ake sa ran zai taimaka sosai wajen saukaka lamura sosai da saukin sarrafa mai wanda kasar gaba daya za ta iya amfana. Kazalika, a karkashinsa ne aka kaddamar da fara hako mai a yankin Bauchi da Gombe lamarin da ka iya zama babban ci gaba ga Nijeriya da dai sauran nasarorin da aka samu a bangaren aikin mai da na gas da kuma sa ran hakan za su taimaka wajen kara samar da hasken wutar lantarki a fadin kasa. Sannan, akwai kaddamar da aikin gas a Ajaokuta-Kaduna da Kano, kaddamar da sabon NPDC a Edo na gas da dai sauransu.
Shugaba Buhari ya taka rawar gani wajen samar da hukumar raya arewa maso gabas, lamarin da ya taimaka wajen farfado da shiyyar bayan da rikicin Boko Haram ya daidaita.
Buhari ya kuma yi amfani da basukan China wajen inganta titi da layin dogo, ya kuma gina sabuwar tashar ruwa a Legas da kammala muhimmiyar gada a kudu maso gabas tare da amincewa da dokokin zabe da na bangaren mai.
Daga cikin kyawawan ayyukan da za a iya duban Shugaban Buhari da su akwai sakan ma sashin shari’a mara domin su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. Buhari ya sha ikirarin cewa ba zai shiga ya yi katsalandan wa tsarin shari’a ba, hakan ya sanya a lokuta da dama ake kallon hakan a matsayin abun da ya dace, amma wasu na suka domin hakan ta bayar da dama wa masu gudanar da harkokin shari’ar na yin sun ransu. Misali an sha samun mutum ko babban jami’in gwamnati balo-balo da rashawa amma haka zance zai kare a labarai ba tare da daukan wani kwararan matakai ba. Hakan dukka ya faru ne sakamakon salon Buhari na kokarin barin bangaren shari’a su gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
Dacin Mulkin Shugaban Kasa Buhari
Ko shakka babu al’ummar Nijeriya da dama ba su tsammaci haka mulkin Shugaba Buhari za ta kare, domin sun zabeshi da tsammani fiye da yadda suka gani. Manyan matsalolin da suka addabi al’ummar Nijeriya a karkashin mulkin Shugaba Buhari kamar yadda bincike ya nuna sun hada da matsalar tsaro, rashawa da cin hanci, wahalar samun mai, tulin basuka.
Ta bangaren matsalar tsaro, a shiyyar arewa maso yammacin kasar nan an samu rahotonnin ta’addancin ‘yan garkuwa da mutane domin neman kudin fansa fiye da tunanin mutum, wannan lamarin ya tada hankalin al’umman kasa har ya sa suka fara yanke tsammanin daga gwamnatin Shugaba Buhari.
Matsalar karancin mai da tada kunno kai a zamanin mulkin Shugaba Buhari: An yi ta samun kwan-gaba-kwan baya dangane da lamarin da ya shafi harkokin sufuri sakamakon yawaitar matsaloli ko karancin samun man fetur da jama’a suka yi ta fuskanta kan dalilai mabanbanta dukka a karkashin mulkin Buhari, lamarin da ya sanya jama’a cikin damuna matuka.
Tulin Basuka:
Binciken masana tattalin arziki da rahotonnin da suka yi ta bayarwa, ya yi nuni da cewa gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta lafto basukan tarihi ma ba zai mance da ita ba. A halin da ake ciki ma, a makon da ya gabata ne Shugaba Buhari ya bukaci majalisar kasa da ta amince masa ya sake ciwo bashin dala miliyan 800 daga bankin duniya, lamarin da ka iya kai wa Nijeriya ya samu kanta a cikin kasar da ake bi bashin dala biliyan 150 a wannan shekarar. Buhari dai ya karbi mulkin Nijeriya ne a gabar da bai wuce dala biliyan 70 ba.
Kazalika, yawan tafiye-tafiye da Shugaba Buhari ya yi jama’an kasa ba za su mance da su ba, domin kuwa an buga misali da cewa shi ne shugaba da ya fi fita kasashen waje walau don jinya ko ziyarce-ziyarce, kan bangaren ziyarartar duba lafiya ana ganin hakan na da nasaba da rashin kayan aiki masu inganci na kiwon lafiya a kasar.
Matsalar tsaro: An yi ta samun matsalar tsaro a kasar nan a karkashin Buhari. Misali, an sace dubban kananan yara ‘yan makaranta tsakanin Disamban 2020 da Satumban 2021, a cewar asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya. An kuma sace dalibai mata 270 daga makarantarsu a Chibok a 2014.
Kisan ‘yan Shi’a a Zariya da sauran wurare, sanin kowa ne an samu rashin jituwa tsakanin almajiran Shaikh Ibrahim Zakzaky da har ta kai an tsareshi na tsawon shekaru. Labarai da aka buga sun ce an samu rikicin ne bayan zargin tare hanya wa tsohon shugaban sojin kasa, Tukur Buratai lamarin da ‘yan shi’an suka karyata.
A cewar ‘yan shi’an, an kashe musu mutane sama da dubu daya, yayin da gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da cewa an bisne sama da ‘yan shi’a dari uku a rami daya bayan wannan rikicin.
Duk bayan rikicin na Zariya, an yi ta samun rahotonnin kisan ‘yan shi’an a lokuta daban-daban da har aka rusa musu gidaje da dama. Wannan ma na daga cikin matsalolin da ake kallon gwamnatin Buhari ta samar.
Wani hari kan wata majami’a a Jihar Ondo da ya kashe gomman masu bauta a shekarar da ta gabata, aya ne daga cikin munanan hare-haren da aka kai.
Mutane da dama suma suna ganin Buhari ya yi kuskure a yadda ya tafiyar da batun jagoran ‘yan aware na IPOB, Nnamdi Kanu.
Bayan ya tsere a 2017, an kama shi tare da tisa keyarsa zuwa gida Nijeriya a 2021 domin fuskantar shari’a. Wani alkali ya bayar da umarnin a sake shi saboda tsarin da aka bi na mayar da shi Nijeriya ba ya bisa doka, sai dai hukumomi sun ci gaba da rike shi.
Masu sharhi sun bayyana gano wani dogon bututu a watan Oktoban bara da ake amfani da shi wajen sace danyen mai a matsayin abin da ba lallai ya yiwu ba ba tare da taimakon hukumomi ba.
A wani waje, barayi sun gina nasu bututun mai tsawon kilomita 4 zuwa tekun Atalantika. A nan jiragen ruwa suna dakon man da aka sato.
Yayin da yake yin bankwana da mulki, za a rika tunawa da yadda Buhari ke tafiyar da tattalin arzikin Nijeriya, saboda yunkurinsa a farkon shekarar nan na sauya fasalin takardun kudin kasar.
Lamarin da ya jefa kasar cikin rudani, yayin da karancin sabbin takardun naira da a yanzu sun bace, ya jefa miliyoyin ‘yan kasar cikin mawuyacin hali musamman kasancewar sun raja’a kan takardun kudin wajen tafiyar da harkokinsu na yau da kullum.
Har ila yau, matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa na daga cikin matsalolin da gwamnatin Buhari ta tarar kuma za ta tafi ta bar shi.
Wasu ma na kallon matsalar karuwa ta yi sakamakon matsaloli da dama, ko da yake a zahirin gaskiya gwamnatin Buhari ta yi kokarin samar da shirye-shiryen da za su samar wa matasa ayyukan dogaro da kai ta karkashin ministan kula da jin kai, amma dai har yanzu akawai matsalar a kasa.