Tsohon ɗan majalisar wakilai na tarayya, Faruk Lawan, ya bayyana cewa zaman gidan yari ya koya masa darusa da dama, ciki har da gane waɗanda ya kamata ya ci gaba da tafiya da su a siyasance.
Faruk Lawan na cikin mutanen da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa afuwa a ranar 9 ga watan Oktoba 2025, bayan amincewar majalisar tarayya.
- Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026
- NPFL Ta Ci Tarar Kano Pillars ₦9.5m, Ta Rage Mata Maki 3 Da Ƙwallaye 3
Lawan, wanda ya wakilci mazaɓar Bagwai/Shanono a Jihar Kano, an yi masa hukuncin ɗaurin shekaru bakwai a gidan yari a shekarar 2021 saboda zargin karɓar cin hanci domin cire sunan wani kamfani daga jerin waɗanda ake zargi da almundahanar kuɗin tallafin mai.
Ya kammala zamansa a watan Oktoban 2024.
A cikin wata hira da BBC Hausa ta yi da shi, Faruk Lawan ya ce yafiyar da shugaba Tinubu ya yi masa ta zama sabuwar dama gare shi don fara sabon babi na rayuwa.
“Idan mutum ya shiga jarrabawa kuma Allah Ya kawo dama ta afuwa, dole ne ya yi farin ciki. Ni da iyalina da masoyana mun yi murna ƙwarai,” in ji Lawan.
“Na gode wa Allah da kuma Shugaba Tinubu saboda ya yi abin da ya kamata a yaba masa.”
Ya bayyana cewa rayuwa a gidan yari ta koya masa juriya da fahimtar cewa komai ƙaddara ce.
“Tun kafin na bar kotu na sallama komai ga Allah. Na sani cewa duk inda mutum ya samu kansa, akwai darasi a ciki,” in ji shi.
Bayan fitowarsa daga gidan yari, Faruk Lawan ya sauya tafiyarsa ta siyasa.
Ya ce ya rabu da tafiyar Kwankwasiyya da aka san shi da ita, duk da cewa har yanzu yana yin zumunci da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
“Shekara guda kenan da na fito daga gidan yari, amma akwai jigo a tafiyar Kwankwasiyya da bai taɓa kira ko taya ni murna ba,” in ji shi.
“A yanzu, siyasa ta faɗaɗa, jam’iyyar NNPP da muka shiga ta yi min ƙanƙanta, don haka dole mutum ya buɗe sabbin hanyoyi.”
Faruk Lawan ya ce yanzu yana son mayar da hankali kan siyasa ta ƙasa baki ɗaya, domin ya koyi cewa jarrabawa na nuna maka waye abokinka na gaskiya.














