Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana yayin taron manema labarai na yau Juma’a cewa, abun da Sinawa suka fi muradi shi ne, zaman lafiya da kwanciyar hankali, kuma tafarkin neman ci gaba cikin lumana, muhimmin zabi ne da ya dace da muradunsu.
Da aka tabo batun wasu na ikirarin Sin tana kara karfi fiye da baya, kuma tana iya zama kalubale ko barazana ga sauran kasashe, sai Mao Ning ta jaddada cewa, har kullum, kasar Sin ta kasance mai neman tabbatar da zaman lafiya a duniya, kuma mai kare odar kasa da kasa, haka kuma, mai bayar da gudunmuwa ga ci gaban duniya.
Ta kara da cewa, ba tare da la’akari da sauyin da duniya ka iya fuskanta ba, Sin za ta ci gaba da fafutukar wanzar da zaman lafiya da ci gaba da hadin gwiwa da moriyar juna, kuma za ta nemi ci gabanta ne yayin da take kiyaye zaman lafiya da ci gaban duniya. Haka kuma, Sin za ta kyautata inganta zaman lafiya da ci gaban duniya ne ta hanyar nata ci gaban. (Fa’iza Mustapha)