Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani, ya ce gwamnatinsa ta fara tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan muhimman kalubalen da jihar ke fuskanta da kuma hanyar samar da zaman lafiya.
Uba Sani ya sake bayyana cewa, zaman lafiya zai dawo ga al’ummomin da ke fama da rikice-rikice da kalubalen tsaro.
- Yadda Fintiri Da Atiku Suka Gudanar Da Bikin Sallah A Adamawa
- Dalibai Sun ‘Yantar Da Fursunoni 6 A Gidan Yarin Suleja
A sakonsa na Babbar Sallah ga jama’an jihar, Sani ya ce gwamnatinsa na bukatar zaman lafiya da kwanciyar hankali domin cimma manufofin gwamnatinsa.
Sani, yayin da ya yaba wa jami’an tsaro da shugabannin al’umma kan ci gaban da aka samu kawo yanzu wajen dawo da zaman lafiya a wasu al’ummomin da ke fama da rikici, ya bukaci kowa da kowa da a sake rubanya kokari don ganin cewa zaman lafiya da kwanciyar hankali ya dawo a dukkanin al’ummar jihar Kaduna.
A wani yanki na sakonsa, Gwamnan ya ce, “Ina mika sakon taya murnar bikin Babbar Sallah ga ‘yan uwana musulmi na fadin duniya. Wannan Idi ne na sadaukarwa da godiya ga Allah madaukakin sarki bisa kyawawan ayyukan da ya yi a rayuwarmu. Muna gode masa don ya sanya mu cikin masu rai a cikin wadannan lokuta masu wuya da ke dabaibaye da kalubale.”