Kamar kowanne mako wannan shafi ya kan zakulo muku batutuwa daban-daban wanda ya shafi al’umma, dantattaunawa akai tare da samun mafita game da abin da ya shafi batun. Tsokacin yau zai yi magana ne game dazamantakewar aure tsakanin miji da mata wa aka fi zalunta?.
Duk da cewa kalmar na da tsaurin gaske ta yaddawasu za su kalli fadin hakan akwai kuskure sakamakon tsaurinta, sai dai wasu ma’auratan na fuskantar matsalolida dama ta bangaren mace ko namiji wanda za a kira shi da zalunci kai tsaye.
- 2023: Za A Fara Shirye-shiryen Aikin Hajji Ranar 21 Ga Disamba – NAHCON
- Adabin Zamanin Da Na Sin (3)
Duk da cewa kai tsaye ba za a kirakowanne bangare da cewar ga wanda ya fi wani ba, sai dai hasashe ta yadda wasu za su iya auna shi a ma’auninaunawa har su hangi wanda ya fi rinjaye da kuma karancin samun ‘yanci.
Kamar yadda wasu mazan za su kalli wasu matan da sun fi maza zalunci musamman wajen take hakkokin da yarataya a wuyansu dan saukewa miji, wanda rashin yinsa zalunci ne da kuma take gaskiya da daukar akasinta, dancimma burinsu da bukatunsu, duk da cewa mazajensu ne, wanda sun riga da sun san da hakan sai dai kawai sutake.
Ya yin da wata macen ba ta iya saurarawa namiji ko raga masa ya zama abin tausayi, tamkar ita ce mijin shine matar.
Haka ma hakkokinsa da ke rataye a wuyanta na bukata ba ruwanta da su face takewa gaskiya da binakasinta, da rashin tsoron Allah, musamman wajen gujewa miji da bin wani namijin daban har a kai da an haifiyaron da ba nasa ba, ya ciyar ya tufatar da shi har ya girma, ba tare da sanin ba dansa ba ne sai ranar da Allah yanufa.
Toh! haka ma yake ga wasu mazan sukan iya take hakokin da ya rataya a wuyansu wajen nisantar zaluntarmatansu, da sauke nauyin da Allah ya dora musu, sun dauki hakan da ba komai ba. Idan aka yi duba da zamani dakuma canjin rayuwa gaba daya, da yawa za a yi ta kallon kowanne bangare dan nemo bakin zaren da inda gizo kesakar, domin kowanne na da nasa matsalar.
Ta yadda wasu matan za su kalli maza da sun fi zalunci ko a wajen sauke hakkin aure ta bangaren bukata ta yaddawasu ba sa iya sauke wa matansu ko da kuwa matan na da bukatarsu har na tsahon wani lokaci ba tare da dalili ba,sai dai su saukewa wasu na waje wanda sam! nauyinsu bai rataya a wuyansu ba.
Da rashin sauke hakkokin cikingida wajen ciyarwa da tufatarwa da sauran abubuwan bukata ko da kuwa mijin yana da abin hannun da zai iyasauke nauyinsa, da hana matan fita neman ilimin da zai taimake su dan rufin asiri, ko neman aikin yi dan rufawakai asiri, bayan hanata duk wasu abubuwan bukata daya kamata ya bata ko da kuwa yana da su, ko fifita mace gudaakan kishiyarta ta bangarori da dama, kamar; barin daya karatu hana daya fita karatu, ko barin guda wajen aiki, ahana dayar yin aiki ko wasu al’amura na cikin gida da dai sauransu.
Ya yin da wasu ke tsintar kansu cikin kunci naduka da zagi ga mazajensu, ba tare da sun aikata laifin hakan ba, face nuna isa da takamar sa na shi ne miji, hadeda ikon juya macen yadda ya so, da rashin sanin darajar aure wanda masu yin hakan ba su sani ba, da dai sauransu.
Akwai matsaloli da dama wanda za a kira su da zalunci kai tsaye, wanda a tawa fahimtar mafi yawan rinjaye hakanna samo asali ne tun daga tushen neman auren ga macen ko ga namijin da za a aura, gami da sanin hakikanin aureda mahimmancinsa, wanda mafi yawa a yanzu ana aure ne domin shagalin aure kawai ba dan sanin abin da za a jeyi ba, sai dan cimma burin kawatuwar wajen shagalin biki da kuma irin shigar da za a yi da abin da za a kashe dakawatuwar tsarin gida da adon cikin gida da bukatar juna da dai sauransu.
Sai dai duk da wadannan abubuwa badukka aka taru aka zama daya ba, akwai zaman auren da babu zalunci ko danasani cikinsa domin an gina shi nebisa tarbiyya da turbar gaskiya da amana da sanin abin da aka je yi na bautar aure, sanin hakikanin auren, wandaa kullum yake samar da farin ciki da walwala a zukata da fuskokin ma’auranta.
Wannan a takaice kenan, bari kumamu ji daga bakin mabiya shafin Taskira game da wannan batu “Ko wa aka fi zalunta a tsakanin miji da mata azamantakewar aure?”.
Ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka:
Sunana Sani Musa Daitu (Jami’in hulda da jama’a Taskar Nasaba) [email protected] 09131227413 Giwa Jihar Kaduna:*
Aure Ibada ne da Allah (S.W.T) ya umurce mu da idan muna da iko mu aura daga biyu, uku ko hudu, idan ba za mu iya ba mu yi daya (Suratul Nisa’i). Sannan sunna ce babba na Manzon Allah (S. A.W), wadda ya yi watsi da sunnar ba shi tare da Manzon Allah. Allah ya saka aure ne ya zama rahama a tsakanin mu domin cika umurnin Allah na saka kalifa a bayan kasa domin yi masa bauta. Sai dai, wasu sun sauya akalar auren zuwa wata fuska wadda muke koyon bakin Al’adu da suke son ruguza mana Tarbiyya da Al’adu masu kyau wadda muka koya a Addini da Al’adun mu, kai tsaye ba za ka iya cewa ga wadda aka fi cuta ba saboda ko wani bangare na da nashi laifin ko gazawar.Mata sun fi cutar da Maza amma saboda rauninsu ya sa wasu ke ganin Maza sun fi cutar da Mata, amma ina son mata su sani Allah Ya sa Maza su zama Shuwagabanni a kansu, kuma daga jikin maza aka fidda su wajibi ne su martaba Namiji ka da su dauka alfarma ce suka yi masa wajen aure, gyara da hani ba cutarwa ba ce a aure, gina nagartacce ahali ne mai Albarka. Dalilansu na da yawa amma abin da ya kawo hakan shi ne, sakin koyarwa addinin Musulunci da Al’adunmu masu kyau da rungumar bakin al’adu wadda ba su dace da mu ba, shi ya haifar da wannan matsalar ta zamantakewar Aure. Bayan haka, Yahudawa sun yaki tunanin mu ta kowacce fuska, mun mayar da su su ne abin koyi ba al’kur’ani da sunnar Manzon Allah (S.A.W) da hanyar magabata na kwarai ba. Abin da yake kawo hakan shi ne; ana yi wa aure shigar sojan badakkare wato babu tsari, Lalacewar Tarbiyya da sakacin Shuwagabanni. Ya kamata a ce a dokar kasa gwamnati ta mayar da hankali a kan gina tarbiyyar aure wadda hakan zai taimaka wajen magance matsalolin da kasar mu take ciki, Idan al’umma ta yi kyau shi ne kasa za ta zauna lafiya. Bayan haka, shiryawa kai Æ™arya da tunanin ban isa a hukuntani ba, ko a barni na yi abin da na ga dama shi ya sa mata da yawa suke ganin maza na zaluntar su, Ya kamata su gane cewa saka su a hanyar da ta dace ake yi. Kasancewar ka namiji ba lasisi ba ne ka zalunci matar ka domin duk abin da ka yi wa wani kai ma za a yi maka. A samar da hukuma ta musamman wadda za ta kula da tsarin zamantakewa na Aure kamar yadda kasashen waje suke yi don tabbatar da ba a zalunci kowa ba, a zamantakewar aure, kuma a hukunta duk wanda ya saba doka, komin girmansa wato doka ta yi aiki akan kowa. A samar da makaranta na kulawa da ma’aurata kamar yadda ake kula da sauran makarantu, a ba wa masana fannin Ilimi Tarbiyya da zamantakewa da malamai na addini kula da Makarantar. Iyaye su sani ‘ya’ya nauyi ne a garesu su tabbata sun ba su tarbiyya irin ta addini, Hadisa “Kowannanku mun ba shi kiwo, kuma za mu tambaye shi kiwon da muka ba shi”, a koyar da samari da ‘yan mata zaman aure tun suna kanana domin zai zo kansu. Shi ne Idan za a yi aure kowa ya nemi kiminsa domin kowacce kwarya da abokiyar burminta, ma’ana shi ne; kowa ya nemi dai-dai da shi ka da a saka karya kuma a bi ka’ida ta addini kuma a nemi zabi gurin Allah ba abin da zuciya take so ba, mafi alheri. Idan za ka kara aure ka tabbata ka cika sharadi wadda addini ya tanada ga wadda yake son zama da mata fiye da daya, Ita ma kuma ta yi hakurin zama da abokiya a gidan aure domin Allah ne ya ce a yi.
Sunana Nabeela Dikko daga Jihar Kebbi:
A ganina an fi zalintar macen, dalilina shi ne; za ki ga komai ke faruwa iyaye da shi kanshi mijin dubin yake ai mace ce, kamar ba ta da wani katabus ko ‘yanci. Dalili ko in ce hujja daya saboda ita macen tana karkashin mijin, kuma kowa ya san macce tana da rauni, to duk da wannan ake amfani ana zaluntar mata a zamantakewar aure. Rashin yi wa mata adalci shi ke kawo hakan ta bangaren mazan da kuma iyaye, za ki ga abu ya faru mace ta dawo gida wasu iyaye ba ma za su yi bincike ba, sai ace ta koma dakinta, da ma zaman aure sai da hakuri da wasu sauran hudubobinsu. To kin ga anan ba a yi wa mace adalci ba, kamata ya yi a saurareta a rarrasheta don babu wanda ya san bakin cikin da take mallaka a gidan aure, sannan shi ma mijin a kira shi a ja mi shi kunne. Amma gaskiya ba ayin hakan wannan yasa maza da yawa ke cin amanar mata kamar dai bayi haka suka mayar da su don sun san matan ba su da tudun dafawa. Hanya daya ce iyaye su shigo ciki su gyara, idan namiji ya yi ba daidai ba a hukunta shi, a baiwa mata ‘yancinsu a dinga yi musu adalci, haka mazan su ji tsoron Allah, su daina kallon mata a matsayin marasa mafita ko kuma wasu marasa ‘yanci.
Sunana Abba Abubakar Yakubu, Marubuci, dan Jarida, (Shugaban Kungiyar Jos Writers Club):
Wannan tambaya ce mai harshen damo, wacce amsar ta kai tsaye yake da wuya. Dalili kuwa shi ne batun zamantakewar aure ba a nuna dan yatsa a ce ga wanda yake cutar da wani, saboda kowanne bangare akwai rawar da yake takawa wajen zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin ma’aurata biyu. Amma idan kai tsaye aka yanke cewa, wa yake zaluntar wani, kenan an nuna namiji ake so a daure domin kuwa an san mace mai rauni ce. Babu wanda zai kalle ta ya yi tunanin tana zaluntar mijinta, sai dai a daidaiku, inda ba a rasa ba. Kamar yadda Bahaushe ke cewa, hannu daya ba ya tafi, haka ma in ana maganar aure to, ba mutum daya ake magana ba. Mata ce da miji!. Kasancewar namiji ne da alhakin rikon iyali da kula da gida, kuma shi ne alkur’ani mai girma ya ambata da mafifici a kan mace, an fi ganinsa a matsayin tushen samuwar adalci, zaman lafiyar iyali, da ci gabansu. Haka kuma idan akasin haka aka samu, ana dora alhakin lalacewar zamantakewar aure kan namiji, wanda shi ne ginshikin gida. Matsalolin zamantakewar aure da rashin fahimtar juna a tsakanin ma’aurata, na samuwa a sakamakon yadda wani bangare ya sarayar da hakki ko nauyin da ke kansa. Kiyaye hakkokin da ke kan miji ko wanda ke kan mata abu ne mai matukar muhimmanci ga dorewar zaman lafiya da fahimtar juna a gidan aure. Matukar miji yana son ya ga daidai a gidansa, tilas sai ya yi kokari ya sauke nauyin da ke kansa daidai gwargwadon iyawarsa. Haka ita ma a bangaren mata, matukar tana son jin dadin gidan aurenta to, ta yi kokarin sauke hakkokin mijinta da ke kanta, gwargwadon karfinta. Yadda a wannan zamani aure ya zama abin wulakantarwa da tozarta, yana daga cikin dalilin da ya sa daraja da kimar auren take zubewa, har aka fara samun masu ganin cewa auren ma ba dole ba ne, ko kuma su rika ganin duk maza halinsu daya, mugaye ne, azzalumai, maciya amana. Ko kuma mazan da ke ganin duk mata halinsu daya, marasa godiyar Allah, marasa kunya, marasa tausayi. Wannan duka kuskure ne, a nawa ganin. Matukar a zamantakewar aure nauyin da ya kamata yana kan namiji shi za a dorawa mace to, tilas kuwa a ga ba daidai ba. Haka idan mace ta sarayar da hakkokinta na kula da miji da bukatunsa, ba za ta ga farin ciki ba. Ubangiji ya yi halittar mace da namiji gwargwadon yadda kowannen su zai iya daukar irin nauyin da aka dora masa. Sai dai kuma bai kyautu mu ce mun tsaya kawai kan hakkokin da aka dora mana ba, domin kuwa addinin Musulunci ya koyar da mu muhimmancin kyautatawa a tsakanin ma’aurata. A inda daya ya gaza hakkin dayan ne ya ga ya tallafa masa. A inda wani ya taimaka, hakkin dayan ne ya nuna yabawa da kyautatawa, don zaman aure ya yi dadi. Mu daina kallon juna a matsayin kishiyoyi ko abokan gasa, kullum kokarin mu shi ne mu ga inda daya ya gaza don mu gallaza masa, ko kuntata masa ko mata, don ya raina kansa ko a ladabtar da shi. Bai kamata ma’aurata su rika ba da dama ko bude kofar da wani zai zalunci wani ko cutar da wani ta gayya, don mugun nufi ba. Mu kyautatawa juna, mu rike juna da amana, da mutuntawa, don mu samu jin dadi da farin ciki a zamantakewar auren mu.
Sunana Abdullahi Muhammad daga Jihar Kano, Karamar hukumar Nassarawa:
Ya daganta da wanne irin zama ake idan na rashin dadi ne, ya danganta da su ma’auratan ma’ana matar ce mara hakuri ko kuma mijin mara hakuri?, Ana samu matar mai hakuri ce amma mijin mara hakuri ta yadda zai yi ta azabtar da ita ta hanya hana ta duk wani hakki da Allah ya dora masa na ta, kamar hanata fita zuwa biki ko suna, rashin yi mata dinki sai bayan kusan shekara ko da kuwa me hali ne idan kuwa mijin ne me hakuri: matar sa za ta fi cutar da shi kasancewar ta san duk abin da tayi masa hakura yake, za ta daina girmama shi, wata ma ko unguwa za ta ba za ta nemi izininsa ba, abin da ke jawo haka akwai rashin ilimin addini musamman rashin ilimin halayyar zaman aure, sannan iyaye ma wasu ba sa nusar da ‘ya’yansu yadda ake zaman aure, Hanyar da za a magance haka shi ne; a nemi ilimin sanin zaman aure, sannan mutum ya yi kokarin auro mai ilimi da tarbiyya.
Sunana Mujittaba Ya’u Ali:
An fi zaluntar miji a zamantakewar aure sosai ma, sun san ya fi hakuri bayan haka kuma shi ne zai je ya nemo amman sai dai a sammasa kuma ya yi magana ace masa ya cika korafi ko kuma ya cika fada, bayan an san ba fada yake ba. Gaskiya mafi yawancinsu son zuciya ne kawai, domin da za ka ce Allah ya sa a yi wa dan uwanta kaninta ko wanta za ka ga ta nuna bacin ranta har ma sai ta yi maka hukunci da baka son danginta. Mu kasance masu gaskiya da rukon amana da kulawa da juna kuma mu cire son zuciya a zaman takewarmu mu kasance masu gaskiya da rukon amana.
Sunana Musbahu Muhammad daga Gorondutse Jihar Kano:
A Wannan zamanin maza sun fi zalintar mata a zamantakewar aure. Maza sun fahimci mata sun yi yawa a gari, suna bukatar mijin aure, suna da son ‘ya’ya, shiyasa wasu mazan suke amfani da yanayin da ake ciki wajan zaluntar matansu. Son rai da rashin sanin darajar aure a musulunce da al’adance. Maza da mata su ji tsoron Allah, su sani cewa aure ibadah me, kuma duk ibadar duniya akwai yadda aka ce a yi ta, sannan za a yi hisabi a tsakanin ma’aurata aranar alkiyama.
Sunana Masa’ud Saleh Doka dawa:
Farko Namiji Allah ya dorawa hikkin kula da duk rayuwar matarsa. Rashin sauke nauyin iyali zalinci ne. Tun mace tana amarya take fara samun zalunci daga miji ba tare da ta gane hakan ba sabida karancin sanin hakki. Wasu mazan suna daukar cewa duk abin da suka ga dama su yi wa matansu dai-dai ne, don an ce gonakinsu ne. Abubuwan dake jawo hakan sune; Karancin ilimin zamantakewar aure a addinance ga maza da matan, karancin biyayyar mata ga mazajensu na jawo musu zalinci ko tauye wani hakkin nasu, Karancin tarbiyya daga iyaye na jawo hakan don sun gani yana faruwa a gidajensu, suma ‘ya’ya suna koyan wannan dabi’un. Karancin hakuri da juriya akan kananun abubuwa na laifi da rashin uzuri ko yafiya ga ma’aurata. Hanyar magance matsalar; Samun cikakken fahimtar juna da halaye kafin aure, Samun wadataccen ilinmin zamantakewar aure a musulunci, fahimtar yadda mata suke tun farkon halittarsu, an yi su ne a karkace, don haka ba za su mike sak! ba, ko ta karfi da yaji. Yawaita nasiha da bin hanyoyin ganarwa daga mazaje, sanin cewa duk abin da kaiwa matarka na kyautatawa ibada ne akwai lada.
Sunana Zinatu Ahmad Isyaku daga Jihar Kaduna:
To Assalamu Alaikum Abin da zan iya cewa anan shi ne; a gaskiya zan iya cewa an fi zaluntar mata. Dalilin da yasa na fadi haka shi ne; na farko namiji na zalintar mace ta bangarori daban kamar rashin bata kulawa, misali rashin abincin da za ta ci, baya kula da ita Idan bata da lafiya, wani mijin ma ya kan toshewa mace hanyar da za ta samu na kanta, idan na ce zan lissafa abubuwan da yasa maza suke zaluntar matansu gaskiya ba zai lissafu ba. To zan iya cewa abin da ke janyo hakan rashin hakuri da kuma fahimta, domin a duk inda za a gina rayuwar aure na farko ka san dole ku kasance masu fahimtar juna da kuma hakuri da juna. Hanyar da za a magance wannan matsala shi ne; ya zamanto kai a matsayinka na mai gida ka sauke nauyin da Allah ya dora maka ita ma matar haka, ya kasance ka bata jin dadi na rayuwa dai-dai misali da kuma su kasance masu hakuri a duk inda suka tsinci kansu.
Sunana Amina Umar Sa’id daga Jihar Kano:
Ni dai na ce mata aka fi zalunta, dalili shi ne; daga cikin wasu mazajen ba sa kulawa da matansu yadda ya kamata, ka ga ba ta yadda za a yi mata ta daga hannu ta ce za ta daki mijinta, wasu mazan ba sa bari matansu su dinga fita, wasu mazan ba sa ciyar da matansu kuma ba sa nuna musu soyayya. Rashin kulawa da rashin nuna soyayya. Maza su dinga bawa matansu lokacinsu, su kuma da za su zauna su tattauna akan matsalolinsu, kuma su bawa juna soyayya.
Sunana Amina Muhammad Sani daga Kaduna:
Gaskiya a nawa ganin an fi zaluntar mata, saboda mace ke daukar duk wata dawainiyar namijin da yara. Rashin yabawa matan da neman musu saukin hidindimu, Janyo su a jiki da yaba wa kokarinsu a ko da yaushe.