Takaddama a jihar Zamfara kan yadda matsalolin sha’anin tsaro ke kara tabarbarewa duk da kokarin da gwamnati da jami’an tsaro ke yi na ganin an shawo kan matsalar na kara daukar sabon salo a bisa ga yadda jigogin siyasar jihar suka fara nunin juna da yatsa.
Gwamna Dauda Lawal wanda al’ummar jihar suke da tsammanin samun zaman lafiya ta hanyar bacci da idanu biyu a karkashin mulkin sa ya zargi tsohon Gwamnann jihar kuma karamin ministan tsaro, Bello Matawalle da hannu wajen daukar nauyin ayyukan ta’addanci da suka kassara jihar mai albarkatun kasa.
A yayin da yake magana a gidan talbijin na TBC, Lawal ya bukaci minsitan da ya yi murabus daga mukaminsa domin ya fuskanci zargin da ake yi masa na daukar nauyin ta’addanci da badakalar kudade a yayin da yake a matsayin Gwamna.
- CMG Da Lardin Jiangsu Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Hadin Gwiwa Ta Tallata Tamburar Hajojin Lardin
- An Kashe Jagororin ‘Yan Bindiga, Sani Black Da Kachalla Makore A Zamfara
“Duk bayanan da muke samu Matawalle yana da hannu a sha’anin ta’addanci nan.
Idan ni ne shi zan ajiye mukami na in fuskanci zargin da ake yi mani har sai na wanke sunana sannan in dawo wa aikina. Wannan shine abin da ya kamata, amma ya za a yi yana da wannan tuhumar a kansa amma kuma har yanzu shine ministan tsaro, hakan ba daidai ba ne.” gwamnan ya bayyana.
Ministan yana shan suka da caccaka kan zargin alakarsa da sha’anin ta’addanci a jihar, lamarin da ya- ki- ci- ya- ki cinyewa wanda ya haifar da dimbin asarar rayuka da dukiyoyi maras misaltuwa.
Tun a baya dai an zargi Matawalle da bayar da kyautar motoci ga jagororin ‘yan ta’adda ciki har da gawurtaccen dan ta’adda Bello Turji ikirarin da Malamin addinin musulunci, Murtala Assada ya tabbatar.
Haka ma Gwamna Lawal ya bayyana cewar tsohon gwamnan ya ajiye ‘yan ta’adda a fadar gwamnati haka ma a na biyan kudin fansa ta hannun gwamnati.
Sai dai a yayin da yake mayar da martani kan zargin da Gwamna Lawal ya yi masa, Matawalle a ranar Talata ya kalubalanci gwamnan da ya fito fili ya yi rantsuwa da Al’kur’ani mai girma kan ba ya da hannu a sha’anin ta’addanci a jihar.
Matawalle ya bayyana hakan ne a gidan talbijin na Channels a cikin shirin Sunrise Daily a inda ya musanta zargin da gwamnan ya yi masa wanda ya nuna yana da hannu a matsalolin tsaro da suka addabi jihar.
Minsitan na tsaro ya tunatar da gwamnan yadda a baya a matsayinsa na jagoran jihar ya yi rantsuwa da Al’kur’ani a kan ba ya da kowane irin hannu a matsalolin tsaro da suka gurgunta jihar da al’ummar ta. Ya ce shi kadai ne gwamnan da yi rantsuwar kuma ya ce idan yana da kowane irin hannu a sha’anin ka da ubangiji ya kara masa dakika daya a duniya.
A cewarsa idan har suna da hujjar da za ta alakanta shi da matsalar ta’addanci, sai su gabatar da ita domin duniya ta ji. Ya ce ko kadan zargin da ake yi masa ba ya da tushe ballantana makama domin abin da ya sani kawai alakarsa da ‘yan ta’adda shine kan yadda ya bukaci sulhu da su domin su aje makamai lamarin da sauran gwamnoni suka dauki irin wannan matakin.
“Ba ni kadai ba ne na yi sulhu da ‘yan ta’adda. Idan za a tuna dukkanin gwamnoni sun yi sasanci da su, gwamnonin Sakkwato da Neja da suka gabata duka sun yi sulhu da ‘yan ta’adda kamar yadda muka yi. Don haka me yasa ni kadai ake zargi?
“Na kalubalanci dukkanin ‘yan siyasa ciki har da Janar Ali Gusau da Dauda Lawal su yi yadda na yi, amma babu wanda ya yi rantsuwar, don haka idan har ba su rantse ba to suna da hannu a ciki.” ya bayyana.
Wannan dai ba shine karo na farko da ake zargin Matawalle da daukar nauyin ta’addanci a jihar ba domin kuwa a Janairu 2020, a yayin da yake a matsayin gwamna a inuwar jam’iyyar APC, jam’iyyar adawa ta PDP ta bukaci ya sauka daga kujerarsa ta gwamna kan zargin hada hannu da ‘yan ta’adda wajen hana zaman lafiya a jihar, zargin da APC ta musanta.
Minsitan a tsakanin 2019 da 2023 ya aiwatar da shirin sulhu da ‘yan ta’adda a yayin da yake a matsayin gwamna, to amma Turji a wani faifan bidiyo a Yuli 2024 ya bayyana cewar an karfafawa wasu abokan ta’addancinsa ne kawai a shirin.
Kafafen yada labarai sun labarta cewar Turji ya bayyana cewar ya kashe daya daga cikin shugabannin ‘yan bindigar daji a karamar hukumarsa ta Shinkafi mai suna Dudu domin a samu zaman lafiya amma kuma daga baya ya yi zargin gwamnan kuma Minsita a yanzu ya yi masa zagon kasa, yana cewar duk wadanda ke zaune a Zurmi da Shinkafi da Isa a Sokoto sun san da hakan.
A yayin da Gwamna Lawal da Minista Matawalle suke ci-gaba da tsayuwa kan kalamansu, jagoran jam’iyyar APC a jihar Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar ya gargadi gwamnan jihar da ya daina dora laifi tare da furta kalaman da ba su kamata ba ga Matawalle.
Yari wanda ke wakiltar Zamfara ta Yamma a Majalisar Dattawa ya bukaci gwamnan da ya yi iyakar kokarinsa wajen shawo kan sha’anin tsaro da ya dabaibaye jihar domin dukkanin gwamnonin da suka gabace shi sun fuskanci kalubalen tsaro kuma sun yi iyakar kokarinsu domin dakile matsalar.
Yari wanda ya shugabanci jihar a tsawon shekaru takwas ya bayyana cewar shine gwamnan jihar na farko da ya fuskanci zazzafan kalubalen sha’anin tsaro amma ya yi abin da zai iya a kokarin shawo kan lamarin.
Ya ce Matawalle ya yi iyakar nasa kokarin domin ganin an samu zaman lafiya a Zamfara ciki har da sasanci da shugabannin ‘yan bindigar dajin kamar sauran gwamnoni na Arewa- maso- yamma, don haka shi ma Dauda ya kamata ya dauki irin wannan matakin maimakon dora alhaki wanda bai kamata ba domin ba zai kawo mafita ga matsalar ba.
A yayin da take tofa albarkacin bakin ta kan lamarin, jam’iyyar PDP a Zamfara ta kalubalanci Sanata Yari kan nesanta Matawalle da zargin matsalolin tsaro da ke addabar jihar.
A jawabin da shugaban jam’iyyar Alhaji Jibo Magayaki Jamilu ya fitar a Gusau ya bayyana cewar mamakon kariya, kamata ya yi Yari ya yi kira da a gudanar da bincike kan duk wani lamari da ya shafi sha’anin tsaron Jihar.
Ya ce ba wai Gwamna Dauda ya yi magana ba ne don dora alhaki ba, sai dai domin bayyana gaskiyar lamari domin ya himmatu wajen raya jihar da magance matsalolin tsaro, lamarin da bai kamata tsohuwar gwamnatin ta ga rashin kokarinsa ba. Jam’iyyar ta kuma ce kamata ya yi Sanata Yari ya mayar da gargadi da shawararsa ga Matawalle domin dukkanin abin da ya shuka shi zai girba.
A makon jiya ne dai jam’iyyar APC a Zamfara ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sanya dokar ta baci a Zamfara domin yaki da ta’addanci a jihar ya samu nasara.
A bayanin da kakakin jam’iyyar Yusuf Idris ya sanyawa hannu, jam’iyyar ta soki gwamna Lawal da yin zagon kasa ga kokarin da gwamnatin tarayya ke yi wajen dakile matsalar ta hanyar farfaganda a kafafen yada labarai.
Sai dai kakakin jam’iyyar PDP a jihar, Halliru Andi ya bayyana cewar jam’iyyar PDP ta tsorata ne da ayyukan raya jiha da ci-gaban al’umma da gwamnan ke aiwatarwa.
Ya ce kiran a sanya dokar ta baci cin fuska ne ga al’ummar jihar wadda tsohuwar gwamnatin ta gurbata al’amurra a mulkin ta wanda a yau Gwamna Dauda ke kokarin saita jihar tare da dawowa da ita saman ingantacciyar turbar ingantaccen mulki.