Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), ta ce mambobinta za su ci gaba da jajircewa wajen ganin cewa jami’o’in gwamnati sun samu abin da suke bukata daga Gwamnatin Tarayya don samun ci gaba da yin takara da jami’o’in kasashen duniya.
Farfesa Ayo Akinwole, shugaban kungiyar ASUU na jami’ar Ibadan ne ya bayyana hakan a jiya Litinin a Ibadan.
- Za Mu Bi Diddigin Yadda Aka Kai Harin Gidan Yarin — Majalisar Wakilai
- Miyetti Allah Ta Roki Soludo Ka Da Ya Soke Kiwon Shanu A Jiharsa
Akinwole, ya ce malaman jami’o’in gwamnati a Nijeriya na amfani da jininsu wajen tafiyar da jami’o’in gwamnati da kuma ci gaba da gudanar da ayyukansu.
“Malamai sun rike jami’o’in gwamnatin Nijeriya da jininsu, amma shin ya dace ‘yan Nijeriya su ce su je su mutu a bakin aiki? Ina sanar da ku cewa suna mu na bin alawus dinmu na sama da shekaru takwas.
“Shin ASUU ne kawai ke yajin aiki? Wasu sassa (cibiyoyin bincike) na kasar nan sun kwashe watanni 13 suna yajin aiki kuma gwamnati na biyansu albashi.
“Shin laifi ne zama malami a jami’o’in Nijeriya? Me ya kai ga yajin aikin? Rashin mayar da hankali ne na gwamnati ya sa aka fara yajin aikin,” inji shi.
A cewarsa, kungiyar ba za ta kasarayar da walwalar mambobinta ba, inda ya nanata cewa zai bijirewa duk wani yunkuri na mayar da masu ilimi zuwa bayi.