Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta mayar da martani kan hirar da dan wasan gabanta Cristiano Ronaldo ya yi da fitaccen dan jarida dan kasar Birtaniya Piers Morgan.
Kyaftin din Portugal din ya yi ikirarin cewa Man United ta ci amanar sa inda ya jaddada cewa baya mutunta kocin kungiyar, Ten Hag.
Sai dai a martanin da kungiyar ta fitar ta shafinta na yanar gizo a jiya ta ce: “Manchester United ta lura da yadda kafafen yada labarai suka yada hirar da Cristiano Ronaldo ya yi.
“Kungiyar za ta mayar da martanin ta bayan tayi nazarin cikakkun bayanai kan hirar.
“Yanzu hankalinmu ya karkata ne kan shirye-shiryen cigaba da samun nasarar wasanni bayan an dawo zagaye na biyu na kakar wasa tare da ci gaba da tabbatar da hadin kai tsakanin ‘yan wasa, manaja, ma’aikata, da magoya baya.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp