Kocin Fc Barcelona Xavi Hernandez ya bayyana aniyarsa na aje aikin horar da kungiyar a karshen kakar wasanni da ake bugawa ta bana.
Xavi wanda tsohon dan wasan tsakiyar Barcelona ne inda ya shafe shekaru da dama a matsayin dan wasa,ya bayyana haka ne bayan rashin nasarar da kungiyar tayi a hannun Villareal da ci 5-2 a ranar Asabar.
- UEFA Champions League: Za Mu Taka Leda Tamkar A Wasan Karshe – Xavi
- Barcelona Ta Shiga Cikin Sahun Masu Neman Daukar Xavi Daga Leipzig
Na tabbata cewa Barcelona gida ne a wajena kuma sun nuna mani kauna a kowane lokaci da na sami kaina a matsayin dan wasa kokuma koci,amma wannan lokaci ne da ya kamata in ajiye wannan aiki inji Xavi.
Tun bayan zuwan Xavi Barcelona ya lashe kofin Laliga 1 da kuka Spanish Super Cup,amma kungiyar na fuskantar kalubale a wasanninta na bana.