Kyaftin din Manchester City Ilkay Gundogan ya koma kungiyar Barcelona, bayan karewar kwanturaginsa a karshen wannan wata kamar yadda kungiyar ta kasar Spaniya ta bayyana.
Manchester City ta gabatar wa Gundogan mai shekara 32, sabon kwanturagi amma ana jin cewa ya daidaita a kan wata yarjejeniya da ta fi tsoka ta tsawon shekara uku da zakarun na kasar Sifaniya.
Kocin Manchester City Pep Guardiola yana alla-alla ya ci gaba da aiki tare da Gundogan, wanda jigo ne a nasarar kungiyar wajen lashe kofi uku a kakar wasan da ta gabata.
Gundogan, dan kasar Jamus mai buga wasa a tsakiya ya buga wasa 51 a kakar wasanni ta 2022 zuwa 2023, inda ya ci kwallo 11 ciki har da kwallayen da ya ci a wasan karshe na gasar FA Cup, inda Manchester City ta doke Manchester United, a ciki har da kwallon da aka ci mafi sauri a tarihin kofin FA bayan dakika 13 kacal.
Ya buga wasa tsawon minti 90 a karawar karshe ta Gasar cin Kofin Zakarun Turai, inda Man City ta ci Inter Milan 1-0, abin da ya sa ta dora a kan nasarorinta na gasar Firimiya da kofin FA a kakar bana.
Gundogan ya shiga kungiyar Manchester City daga Borussia Dortmund a kan kudin da aka ba da rahoto sun kai fam miliyan 20 a shekara ta 2016, kuma ya buga wa kungiyar wasanni 304, ya ci kwallo 60 sannan ya taimaka aka zura guda 40 a raga.
A tsawon shekara bakwai da ya kwashe a filin kwallo na Etihad, ya ci kofi 14 – Gasar Firimiya biyar da Gasar Zakarun Turai daya da Kofin FA biyu sai Kofin EFL guda hudu da kuma Community Shields biyu.
A farkon kakar 2022 zuwa 2023 ne Man City ta nada shi matsayin kyaftin bayan dan wasan tsakiyar Brazil Fernandinho ya bar kungiyar kuma zamansa kyaftin ya kawo wa kungiyar gagarumar nasara.
A karshe dai, lamarin ya kare cikin wani sassaukan lissafi daga yadda Man City ke kallon lamarin saboda suna son Gundogan ya ci gaba da zama amma kuma sun girmama matakin da ya dauka na son tafiya.
Guardiola ya yi ta zazzaga wa Gundogan kalmomin yabo musamman a makonnin
karshe na kakar wasannin mai cike da tarihi a kungiyar ta Manchester City sai dai City ba za ta iya kashe ko nawa ba ne, don kawai tana so ta ci gaba da zama da Gundogan.
Zakarun na Ingila da Turai sun yi masa tayin kwanturagin shekara daya da yiwuwar karin kakar wasanni amma Barcelona ta yi masa tayin da ya kunshi karin shekara daya a kan na Manchester City.
Gundogan yana da shekara 32, kuma zakakurin dan wasa a City, yana sane da cewa ‘yan kwallo kafar ne za su iya gasa da shi kuma Man City, a matsayin kungiyar da ta yi nasarar cin kofi uku, suna kan sharafinsu.
‘Yan wasa a yanzu na son zuwa su buga kwallo da Guardiola.
Kungiyar za ta iya samun zaratan ‘yan baiwa, kuma ko Kobacic, yana daf da yin haka sai dai Man City cikin bege za ta rika tunawa da Gundugan tamkar dai David Silva da Yaya Toure da kuma Vincent Kompany.