• English
  • Business News
Tuesday, November 4, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zan Ci Gaba Da Inganta Birane Da Karkara – Gwamna Bala

by Khalid Idris Doya
3 years ago
Gwamna Bala

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Muhammad ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da samar da ayyukan raya kasa da samar da romon dimokuradiyya a birane da karkara da nufin yaki da fatara, wahalha da zaman kashe wando don ciyar da al’umma baki daya.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a fadar shugaban kasa a birnin tarayya, yayin amsar lambar yabo daga cibiyar TBS da hadin guiwa da ofishin sakataren gwamnatin tarayya kan ayyukan sa na raya kasa da gina yankunan karkara.

  • Shugaban Karamar Hukuma Ya Rufe Otal Kan Aikata Ayyukan Badala A Kebbi
  • Zan Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Kamar Yadda Buhari Ya Yi – Tinubu 

Hadimin Gwamnan kan sabbin kafafen sadarwa, Lawal Mu’azu ya nakalto gwamnan na cewa lambar yabon za ta kara masa kumaji da haxaka wajen zage damtse domin hidimta wa jama’a.

Da ya ke sadaukar da lambar yabon da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika masa ga ɗaukacin al’ummar jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya ce za ta kara masa karfin guiwa wajen cigaba da ayyukan jin kai kana yayi kira ga al’umma da su cigaba da marawa

gwamnatinsa baya don kai ga nasara musamman a sashen kiwon lafiya, hanyoyi da ingantaccen ilimi.

LABARAI MASU NASABA

Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja 

Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

Gwamnan ya samu rakiyar uwargidan sa Aisha Bala Muhammad, shugaban jam’iyyar PDP reshen jiha, Ƙoshe Hamza Akuyam da Honorabul Auwal Jatau.

Saura sun hada da kakakin majalisar dokoki ta jiha Abubakar Suleiman da tsohon mataimakin gwamna Audu Sule Katagum.

Tun da farko Kakakin gwamnan Mukhtar Mohammed Gidado, ta cikin wata sanarwar da ya fitar, ya ce wannan lambar yabon kari ne kan wasu da dama da gwamnan ya samu bisa jajircewarsa wajen tabbatar da kai jihar Bauchi zuwa mataki na gaba.

Sanarwar ta ce, yadda gwamnan ya hummatu wajen shimfida ayyukan raya jihar ta birane da karkara, kiwon lafiya, gona, tsaro, samar da ayyukan dogaro da kai, da sauransu suna daga cikin fannonin da masu bada lambar yabon suka duba wajen karrama gwamnan.

LEADERSHIP Hausa dai ta labarto cewa gwamna Bala Muhammad na daga cikin mutum 44 da suka amshi lambar yabon daga hannun Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Juma’a.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Jami’an Tsaro Sun Dawo Da Fasfo Ɗin Sanata Natasha Bayan Ƙwace Shi A Abuja
Manyan Labarai

Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja 

November 4, 2025
Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo
Manyan Labarai

Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

November 4, 2025
Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 
Manyan Labarai

Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

November 4, 2025
Next Post
Da Dumi-Dumi: Maharan Da Suka Farmaki Sanata Ufeanyi Ubah Sun Shiga Hannu

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

November 3, 2025
Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

November 3, 2025
An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

November 3, 2025
“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump

“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump

November 3, 2025
Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai

Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai

November 3, 2025
Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka

Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka

November 3, 2025
Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya

Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya

November 3, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.