• English
  • Business News
Monday, November 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zan Ci Gaba Da Yaki Da Cutar Daji Da Matsalolin Mata -Dakta Zainab

by Bushira Nakura
3 years ago
Dakta Zainab

Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Zainab Shinkafi Bagudu ta yi alkawarin ci gaba da yaki da cutar daji ko da bayan ta bar mulki.

Dakta Zainab dai, wacce kuma ita ce shugabar gidauniyar Medicaid Cancer Foundation ta bayyana hakan a Birnin kebbi a wani taron tattaunawa da ‘yan jarida a wani bangare na kokarin ganin ta samu nasarar gudanar da aikinta daga shekarar 2015 zuwa yau.

  • Sin Na Fatan Amurka Za Ta Yi Gamsasshen Bayani Game Da “Nord Stream”
  • Matsalar Tsaro Ta Haifar Da Koma-baya A Jihohin Arewa  —Masari

A cewarta, ” cutar daji za ta ci gaba da ta’azzara. Za ta ci gaba da karuwa kuma ana bukatar karin Ma’aikatan da za su gudanar da  aiki don magance matsalar cutar daji.

”Har ila yau, akwai rashin daidaituwa a cikin ayyukan da ake bukata da kuma isassun kudi. Ya kamata a ga ciwon daji a matsayin matsala da za a baiwa muhimmanci da  gaggawa.

“Zan ci gaba da gudanar da ayyukana na tuntubar jama’a don gudanar da yekuwar  da wayar da kan jama’a da ake bukata ta hanyar tattaunawa da masu ruwa da tsaki na jaha da na kasa baki daya.”

LABARAI MASU NASABA

Ko Kin San… Maganin Sanyi Na Mata (Infection)?

Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?

Haka Zalika, Dakta Zainab Bagudu ta ci gaba da cewa, gwamnati da masu ruwa da tsaki a shirye suke su dauki matakin gaggawa domin dakile yaduwar cutar.

Ta yi alkawarin yin aiki tare da gwamnati, kungiyoyi farar hulla da duk masu ruwa da tsaki don kara yawan kudade don yaki da cutar daji, tare da samar da matakan rigakafi.

”Wannan babbar matsala ce a Nijeriya kasancewar kasar ba ta yin abin da ya dace idan aka yi la’akari da yawan al’ummar kasar.

Har ilayau, “Hadin gwiwa mai karfi yana da matukar mahimmanci ta wannan hanyar kamar yadda tsarin tuntubar kasa shima yana da mahimmanci.

Ta ce “Jihar Kebbi ta yi abubuwa da yawa. Muna da tsarin kula da cutar kansa da kuma asusun kansa na marasa galihu.

“Haka kuma akwai tsarin inshorar lafiya musamman a matakin PHC kuma dole ne mu kara himma wajen samar da karin ayyuka,” in ji Dakta Zainab Shinkafi Bagudu.

Ta yi godiya ga maigidanta Gwamna Abubakar Atiku Bagudu   da duk masu ruwa da tsaki bisa yadda aka amince da dokar kare hakkin yara da mata a jihar Kebbi.

Sun hada da dokar BAPP, dokar kare hakkin yara da kuma dokar GBB, inda suka ce matakin da gwamnatin jihar karkashin jagorancin maigidanta Abubakar Atiku Bagudu ta yi abin yabawa ne matuka.

Daga nan ta jaddada bukatar jama’a musamman wadanda aka zalunta da iyayen wadanda aka yi wa fyaden su rika fadin albarkacin bakinsu tare da kai rahoton irin wannan lamari.

”Ya kamata jama’a su dauki matakin da ya dace kuma su samu hujjojin da suka dace. Yakamata kuma a dage da wayar da kan jama’a,” in ji ta.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?
Adon Gari

Ko Kin San… Maganin Sanyi Na Mata (Infection)?

October 19, 2025
Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?
Adon Gari

Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?

October 12, 2025
tusar gaba
Adon Gari

Ko Kin San… Dalilin Da Ke Sa Mata Ke Ganin Farin Ruwa Kafin Ko Bayan Al’adarsu?

August 31, 2025
Next Post
Yadda ‘Yan Nijeriya Ke Shirye-shiryen Shigowar Watan Azumi

Yadda ‘Yan Nijeriya Ke Shirye-shiryen Shigowar Watan Azumi

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno

Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno

November 10, 2025
Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

November 9, 2025
An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

November 9, 2025
Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

November 9, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

November 9, 2025
CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

November 9, 2025
Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

November 9, 2025
Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

November 9, 2025
Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

November 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.