Dan takarar zama gwamnan jihar Kaduna a jam’iyyar APC, Sanata Uba Sani, ya yi alkawarin ci gaba da ba harkar ilimi fifiko idan har aka zabe shi ya zama gwamna a zabe mai zuwa.
Uba Sani, ya ce, “Gwamnatin PDP ta yi watsi da makarantun gwamnati a cikin shekaru 16 da jam’iyyar ta yi tana mulki, ya yi alkawarin ci gaba daga inda gwamna Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya tsaya, musamman bangaren inganta ilimi, idan ya samu damar zama gwamna.”
Sanatan ya bayyana haka ne a wurin taron kaddamar da yakin neman zaben sa a garin Giwa da ke jihar Kaduna a ranar Talata, 17 ga Janairu, 2023.
Dan takarar gwamnan wanda ya ce gwamna El-Rufai ya dawo da martabar da aka rasa a makarantun gwamnati, ya ce: “Abin da na sa a gaba shi ne na samar da ingantaccen ilimi ga ‘yan’uwa talakawa domin hakan ne zai ba su damar samun kyakkyawar makoma da kuma inganta al’umma gaba daya.”
Haka kuma yi alkawarin karfafa malaman addini tun kafin zaben gwamna na 2023 a jihar, inda ya kara da cewa su na taka muhimmiyar rawa wurin gyara al’umma.
Dan takarar gwamnan ya gode wa al’ummar karamar hukumar Giwa bisa goyon bayan gwamnatin APC a matakin tarayya, jiha da kananan hukumomi.
Ya kuma ce, “Ayyukan da aka aiwatar a cikin karamar hukumar Giwa ba za su yiwu ba idan ba tare da tallafin ku ba. Ina so ku ci-gaba da mara wa jamiiyar APC baya ta hanyar zaben jam’iyyar mu a dukkan matakai a zabe mai zuwa,” in ji shi.
Da ya ke jawabi a wurin gangamin, Gwamna Malam Nasir El-Rufai ya bukaci al’ummar Giwa da su zabi Sanata Uba Sani a matsayin magajin sa da kuma Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe a matsayin mataimakiyar sa saboda su na cikin tawagar su ka taimaka wurinn kawo sauyi a jihar Kaduna a karkashin jagoranci na.
Gwamnan ya kuma umarci jama’a da su zabi Muhammad Sani Abdullahi (Dattijo) a matsayin sanata mai wakiltar shiyya ta biyu da Honarabul Bashir Zubairu a matsayin dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Giwa da Birnin Gwari.
Ya kuma bukace su da su zabi ‘yan takarar mazabar Giwa ta Gabas da Yamma.
A yayin kamfen din, Mataimakiyar gwamnan ta kaddamar da cibiyar kula da mata masu juna biyu yayin da El-Rufai ya kaddamar da cibiyar wasanni na Unguwa gabanin taron.
Gwamna Nasir El-Rufa’i Sanata Uba Sani, mataimakiyar gwamna Hadiza Sabuwa Balarabe da sauran jami’an gwamnati sun kuma gana da masu ruwa da tsaki, inda suka gabatar da tambayoyi tare da bayyana wasu manufofin gwamnati.