Assalamu Alaikum Allah ya kara wa Dr. lafiya, ina da tambaya: Shin ya halatta mutum ya shafa ‘cream’, domin gemunsa ya fita ya tsayar da SUNNAH?
Wa alaikum Assalam, zai fi kyau ya jira har Allah ya fito masa da shi, saboda amfani da magungunan da suke canza yanayin Dan’adam yana biyar da matsaloli a mafi yawan lokuta.
Allah yana iya ba ka ladan wanda ya tsayar da gemu ko da bai fito ba, mutukar niyyarka ingantacciyya ce.
Allah ne mafi sani
Ko Zan Iya Bai Wa Kannena Zakka?
Assalamu alaikum, Malam ko ya halatta in ba ma’aikatana da kannena zakka?
Wa alaikum assalam.
To dan’uwa ba ya halatta musulmi ya ba da zakka ga wadanda wajibi ne a kansa ya ciyar da su; kamar iyaye maza da mata, kakanni; maza da mata, da kuma ‘ya’ya da ‘ya’yan-‘ya’ya; saboda ba da zakka ga wadannan zai sauke masa nauyin ciyar da su da ya ke wajibi a kansa; daga nan kuma sai amfanin ba da zakkar ta dawo kansa.
Amma kanne kuwa, to ciyar da su bai wajaba a kanka ba, don haka ya halatta ka ba su zakka, haka nan ma’aikatanka.
Sannan daga cikin ka’idojin da malamai suke fada a wannan babin shi ne duk mutumin da idan ka mutu ba zai gaje ka ba, to ya halatta ka ba shi zakka, ka ga kuwa kanne ba sa gado mutukar akwai ‘ya’ya.
Duba fikhul-muyassar shafi na: 145
Allah ne mafi sani.