Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce zai ware Dala biliyan 10 domin magance matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasar Nijeriya a zaben 2023 mai zuwa.
Atiku ya bayyana hakan ne a Ilorin, babban birnin Jihar Kwara a wajen kaddamar da yakin neman zaben jam’iyyar PDP na Arewa ta Tsakiya, wanda aka gudanar a dandalin Ilorin.
- Yadda ‘Yan Majalisa Suka Bai Wa Hammata Iska A Saliyo
- Matsalar Karancin Man Fetur Na Ci Gaba Da Ta’azzara A Legas
Tsohon mataimakin shugaban kasar nan, ya ce za a yi amfani da kudin ne wajen taimaka wa matasan Nijeriya wajen kafa kanana da matsakaitan masana’antu.
“Ina so in tabbatar muku da cewa rashin aikin yi da matasa ke fama da shi a duk fadin kasar nan ba a iya Jihar Kwara ko shiyyar Arewa ta Tsakiya ya tsaya ba, yawancin ku a nan ‘yan kasa da shekara 30 ne kuma yawancin ku a nan ba su da aikin yi ko sana’a. Za mu tabbatar da cewa a cikin shirin namu na yi alkawarin cewa zan ware Dala biliyan 10 don ganin an samar da ayyukan yi ga matasa a kananan da matsakaitan sana’o’i don ba ku dama da kuma tabbatar da cewa an samar muku da ayyukan yi.
“Ba mu zo nan don mu muku karya ba, mu iyayenku ne, muna son ku zama kamar yadda muke, za mu ba ku dama, za mu kawo ku, za mu tabbatar kun cimma burinku, ko mene ne. Babban burin ku, shi ya sa muke nan, kar ku sake zabar APC, ku zabi duk ‘yan takarar PDP a 2023.
“Mun kuma yi alkawarin dawo da tsaro a duk fadin kasar nan, lokacin da suka zo sai suka ce za su magance matsalar rashin tsaro nan a watanni shida, amma me muke gani? abubuwan da ke faruwa,” in ji Atiku.
Dan takarar shugaban kasar ya bukaci ’yan Kwara da su zabi dukkan ‘yan takarar PDP a zaben 2023 mai zuwa.
Atiku, wanda ya ce a ranar Laraba ne jam’iyyar ta kaddamar da kwamitin mata na PDP, ya kara da cewa ita ce ta farko a tarihin babbar jam’iyyar adawa.
Ya yaba wa al’ummar Jihar Kwara bisa yawan fitowar jama’a tare da gode musu bisa goyon bayan da suka samu da kuma tarbar da tawagar yakin neman zabensa suka yi.