Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP Alh Atiku Abubakar, ya yi alkawarin cewa, zai tabbatar da hada kan kasar nan duk da cewa gwamnatin APC mai ci, ta riga ta raba kan ‘yan kasar.
Wazirin Adamawa, ya bayyana hakan ne a garin Asaba a yayin taron yakin neman zabensa da mataimakinsa Okowa, inda ya ce, idan PDP ta kai ga tudun na tsira za ta tsamo kasar daga halin da ta tsinci kanta a yau.
Ya ce, ba wai yazo jihar Delta yin gangamin yakin neman zabe ba ne, ya zo ne don ya nuna godiyarsa ga al’ummar jihar, inda ya yi alkawarin cewa, ba zai ci amanar su ko juya musu baya ba, musamman ganin cewa, ‘yan jihar ba su taba gaza wa akan zabensa ba.
Atiku ya kara da cewa, a sabida haka ne yasa na dauko Okowa don ya yi min mataimaki, inda ya bukaci ‘yan jihar da su ci gaba da marawa Okowa baya, musamman ganin cewa, shine zai kasance a gobensu.
A cewarsa, tun a shekarar 1999 jihar ta kasance, jihar magoya bayan PDP, saboda haka baku da wani dalilin goya wa wata jam’iyya baya.