Tsohon mataimakin shugaban kasar Nijeriya kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ware dala biliyan 10 domin inganta rayuwar matasa da iliminsu.
Ya bayyana haka ne a filin wasa na UJ Esuene a Kalaba, a lokacin da yake jawabi ga dimbin magoya bayan jam’iyyar PDP, gabanin shiga zaben shugaban kasa.
- Gwamnatina Za Ta Tabbatar An Fara Hako Mai A Bauchi Da Gombe – Tinubu
- Jami’an NIS Na Rundunar JTF 60 Sun Samu Karin Girma Kai-tsaye A Maiduguri
Ya ce, idan aka kada kuri’a a kan mulki, tsaro da abubuwa biyu ne za su sa a gaba a gwamnatinsa.
Atiku ya ce, “Za mu ware dala biliyan 10 domin ilmantar da matasanmu da kuma ba su horo ta yadda za mu kawar da talauci da aikata laifuka. Da wannan ne za a samar da ayyukan yi kuma rashin tsaro a kasar nan zai ragu matuka.”
Don haka Atiku ya yi alkawarin ba shakka gwamnatinsa za ta sauya fasalin kasar nan, inda ya kara da cewa za a dauki hakan a matsayin babbar manufar gwamnatinsa.
“Za mu matsa don sauya fasalin kasar nan a matsayin babbar manufar gwamnatin PDP mai zuwa ta hanyar rage karfin gwamnatin tarayya da bai wa jihohi da kananan hukumomi dama, ta yadda za mu dora alhakin dukkan shugabanninmu na kowane mataki na gwamnati.
“Hakan zan sa Gwamnatin Tarayya ta yi kasa a gwiwa sannan kuma za a tura manyan mukamai da kayan aiki zuwa jihohi domin amfanin al’ummarmu,” in ji shi.
“Bari na kuma tabbatar muku da cewa da jam’iyyar PDP, amfanin gonakinku zai kasance abu mai amfani tare da hanyoyin sadarwa zuwa kasuwannin kasashen waje.”
Ya yi nuni da cewa shekaru takwas ‘yan Nijeriya suna sha wahala sakamakon gazawar jam’iyya mai mulki.
Da yake jawabi tun da farko, Shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu, ya yi kira ga al’ummar jihar da su zabi PDP domin su kwato wa ‘ya’yansu ‘yanci.