Rundunar ‘Yansandan Babban Birnin Tarayya ta tabbatar da cafke Fasto Uche Aigbe na cocin Rock cathedral wanda ya hau kan mimbari da AK-47 a ranar Lahadi.
Hoton faston cocin ya karade shafukan sada zumunta.
- Gwamnatina Za Ta Tabbatar An Fara Hako Mai A Bauchi Da Gombe – Tinubu
- Kasare Sin: Amurka Ce Kan Gaba Wajen Leken Asiri Da Sanya Ido Da Na’urori
An hange shi yana wa’azi a cocin da bindiga kirar AK-47 a rataye a kafadarsa.
Kakakin rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya Abuja, DSP Josephine Adeh, wanda ta tabbatar da kamen a wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, ta ce an kama faston ne tare da wani Insifeto Musa Audu wanda ya ba shi bindigarsa.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “An kama faston wanda sakonsa da zanga-zangarsa na tunzura jama’a ne a safiyar ranar Litinin tare da babban jami’in tsaro na cocin da kuma wani Sufeto Musa Audu wanda ke bakin aiki a ranar wanda ya yi wasarere bindigarsa ba bisa ka’ida ba.
“An fara gudanar bincike, ana kira ga jama’a da su yi watsi da ayyuka ko maganganun da suka saba wa dokokin da suka dace saboda doka kuma duk masu karya doka za a hukunta su.”
Faston dai ya dauki bindiga kirar AK-47 ya shiga cocin da yake wa’azi rataye a kafadarsa a ranar Lahadi, lamarin da ya bai wa dubban mutane mamaki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp