Shugaban kasa Bola Tinubu ya yaba da zaben Godswill Akpabio da Tajudeen Abbas a matsayin shugaban majalisar dattawa da shugaban majalisar wakilai, inda ya tabbatar da cewa zai yi aiki a fili tare da sabbin shugabannin majalisar.
Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa a ranar Talata, inda ya bayyana nasarar shugabannin majalisar guda biyu da mataimakansu, Jibril Barau da Benjamin Kalu a matsayin babban ci gaban da aka samu a cikin dimokuradiyyar Nijeriya.
- An Cafke Mai Sojan Gona A Matsayin Jami’in EFCC Da Sojoji
- ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Daliban Jami’ar Jos 7
Tinubu ya ce, “A matsayina na shugabanku a shirye nake in yi aiki tare da majalisar dokoki ta kasa a bayyane. ‘Yan Nijeriya na sa ran manyan sanatoci da ‘yan majalisar wakilai za su kafa dokoki da gudanar da ayyukan sa ido da za su inganta ayyukan gwamnati don samun sakamako mai kyau ciki har da inganta rayuwarsu.
“A yayin aikinmu tare, ana iya samun rashin jituwa. Idan ba mu yarda da haka ba, to za mu yaudari kanmu, rashin son zuciya da neman rage wa majalisar dokoki ta kasa ko wani mamba ba zai taba haifar mana da da mai ido ba.”
Shugaban ya tunatar da su cewa, zaben da takwarorinsu suka yi masu a matsayin shugabanni da kuma dora ragamar shugabancin majalisar babban abin alfahari ne da ke tattare da gagarumin nauyi tare da fatan za su ba da marasa kunya wajen aiki kafada da kafada da sauran ‘yan majalisa da kuma daukacin ‘yan Nijeriya.
Ya jajanta wa Abdulaziz Yari da Idris Wase da kuma Aminu Jaji wadanda suka fadi zabe bisa inganta tsarin shugabanni majalisa ta 10. Ya yi kira gare su da su ci gaba da gajircewa kamar yadda suka yi a takarar shugabancin majalisar dokokin kasa wajen gudanar da ayyukansu ga al’ummar mazabarsu da kuma Nijeriya.
Tinubu ya taya daukacin ‘yan majalisar dokoki ta kasa wadanda a suka shiga aikin yi wa al’ummar kasar nan hidima.
Ya gargade su da cewa, “Muna yin kira ga dukkaninmu mu yi kokarin sauke nauyin da ke kanmu da kuma amfani da rantsuwar da muka yi na hakkin hidimta wa kasarmu. Lokaci ya yi da za mu ci gaba da tafiya tare wajen gudanar da harkokin mulki domin ci gaban Nijeriya.
“Mutane a fadin kasar nan suna sa rai sosai daga gare mu. Suna son mu sauke nauyinsu na tattalin arziki. Suna son mu kawar da rashin tsaro domin manomanmu na karkara su je gonakinsu su noma abincin da muke ci.”
“Mutanenmu sun zuba mana ido mu gyara arzikin kasarmu da kuma kawar da duk wani shingen da ke hana ci gaba. Duk wadannan za mu iya yi ne kadai idan muka jajirce. Za mu iya cimma dukkan kyawawan abubuwan da muka alkawarta a lokacin yakin neman zabe idan muka yi aiki tare cikin jituwa da mutunta hakkinmu da kuma maslahar kasarmu.
“Ba za mu yi watsi da wannan damar ba saboda ‘yan Nijeriya suna son mu yi amfani da kowace rana a cikin shekaru hudu masu zuwa. A bisa lamarin gaskiya, mutanenmu suna son mu rubayya kokarin gwamnatinmu. Hakika sun cancanci shugabanci nagari mai cike da adalci wanda zai inganta rayuwarsu. Dole ne mu ba su iya abin da zamu iya.
“Zan ci gaba da abokin kowa don samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaban Nijeriya. Ina kira ga shugabannin majalisar dokoki ta kasa ta 10 da dukkan ‘yan majalisa su yi aiki tare da ni a wannan tafiya ta gwamnati.”