Zababben gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya ce ba ya wata tantama shi ne zai yi nasara a kotu matukar jam’iyyar adawa sun kalubalanci sakamakon da ya ayyana shi a matsayin zababben Gwamnan jihar.
Uba Sani ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da kamfanin BBC Hausa ya yi da shi.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ce ta ayyana Uba Sani a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gabatar a ranar Asabar din da ta gabata bayan ya yi galaba a kan Isa Ashiru na jam’iyyar PDP.
In ba a manta ba dai, zaben tsakanin ‘yan takarar biyu ya yi zafi sosai inda aka yi ta jan lokaci kafin sanar da sakamakon.
A hirarsa da BBC Hausa Aliyu Abdullahi Tanko, Sanata Uba Sani ya ce zai yi mulki tare da kowa kuma zai rike amanar da al’ummar jihar Kaduna suka damka masa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp