Shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin zagon kasa (EFCC), Ola Olukoyede ya sha alwashin bin diddigin batun gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello har zuwa karshe.
A hirarsa da manema labarai a hedikwatar EFCC da ke Jabi a Abuja a ranar Talata, ya sha alwashin sauka daga kan kujerarsa matukar ba a gurfanar da Yahaya Bello ba.
Ya kuma yi alwashin hukunta dukkanin wadanda suka yi kokarin kawo matsala wajen hana cafke tsohon gwamnan na Kogi.
EFCC na kokarin gurfanar da Yahaya Bello ne kan tuhume-tuhume 19 da ke da alaka da zargin halasta kudaden haram, cin amana, almundahanar sama da Naira biliyan 80.
Olukoyede, ya ce EFCC na bukatar goyon bayan ‘yan Nijeriya domin samun nasara ayyukanta.
Ya kara da cewar kokarin da hukumar ke yi a yanzu ya taimaka wajen farfado da darajar Naira da kasuwar musayar kudade.
A makon da ya gabata ne, Yahaya Bello ya shiga wasan buya tsakaninsa da EFCC, wanda hakan ya sanya ta ayyana nemansa ruwa a jallo.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp