Ƙanwar Sakataren Gwamnatin Jihar Kano (SSG), Dr. Baffa Bichi, Hajiya Lami, ta sanar da ficewarta daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.
Hajiya Lami ta bayyana wannan matakin ne a lokacin taron da aka gudanar a gidan Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, a Abuja, tare da alwashin jawo ɗan uwanta, Baffa Bichi, zuwa jam’iyyar APC.
- Turkashi: Aisha Bichi Ta Ce Jami’an Tsaron Farin Kaya Su Kamo Mata Abba Gida-Gida
- Da Dumi-dumi: Tinubu Ya Maye Gurbin Bichi Da Ajayi A Matsayin Shugaban DSS
Baffa Bichi, tsohon Babban Sakataren Asusun Tallafawa manyan makarantu (TetFund) a zamanin Shugaba Muhammadu Buhari, ya zama Sakataren Gwamnatin Jihar Kano ne bayan naɗin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi masa ranar 30 ga Mayu, 2023.
Sanata Barau, wanda ya kayar da Baffa a zaɓen Sanatan Kano ta Arewa a 2023, ya marabci Hajiya Lami da ‘yan wasu ƴan jam’iyyar zuwa APC.
Hajiya Lami, wacce ta kasance mai jagorantar mata a siyasa, ta ce,
“A yau, tare da abokan siyasa ta, mun bar NNPP don haɗa kai da APC domin magance matsalolin da ke addabar jiharmu da ƙasarmu. Zan kawo ɗan uwana, Baffa Bichi, zuwa APC nan bada daɗewa ba.”
Sanata Barau ya tabbatar da cewa jam’iyyar APC za ta tabbatar da adalci ga dukkan mambobinta tare samar da cigaban Nijeriya a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu.