Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun cafke daya daga cikin jagororin zanga-zangar kuncin rayuwa da ake yi a babban birnin tarayya, Micheal Lenin.
Hukumar DSS ta kama Lenin da misalin karfe biyu na safiyar ranar Litinin a gidansa da ke unguwar Apo a babban birnin tarayya Abuja.
- Gwamnan Filato Ya Ƙaƙaba Dokar Hana Fita Ta Awa 24
- Jami’in Zimbabwe Ya Yabawa Kamfanin Kasar Sin Da Ya Goyi Bayan Ajandar Bunkasa Masana’antun SADC
Da yake magana da jaridar Punch, Daraktan tafiyar ‘Take It Back Movement’, Damilare Adenola, ya ce jami’an DSS sun kai farmaki gidan Lenin.
Ya kuma yi zargin cewa, DSS ta kuma ci zarafinsa a lokacin da suka kama shi.
Adenola ya ce, “Hukumar DSS ta kama Lenin a wani samame da aka kai gidansa da misalin karfe biyu na safiyar Litinin.
“An kama shi tare da azabtar da shi a gaban iyalinsa. Muna neman a sake shi ba tare da wani sharadi ba.”
Ba a samu damar jin ta bakin mai magana da yawun hukumar DSS ba, Peter Afunanya har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton.
Lenin, wanda shi ne Babban Kodineta na Kasa, na Yakin Kare Hakkokin Matasa, na daya daga cikin wadanda suka shirya taron da suka yi magana a taron manema labarai inda suka nuna rashin jin dadinsu da jawabin da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa ‘yan kasa kan zanga-zangar da ake gudanarwa a fadin kasar a ranar Lahadi.
A jawabin da ya yi, ya ce, jawabin da shugaban kasar ya yi, ya nuna cewa, bai san ma me ke faruwa ba a kasar.