Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Maru/Bungudu a jihar Zamfara, Alhaji Abdulmalik Zubairu (Zannan Bungudu), ya gyara tare da gina masallatan Juma’a guda 20 a makarantun islamiyya 15 a Kananan Hukumomi Maru da Bungudu.
Da yake zagaya da ‘yan jarida domin duba ayyukan, mataimaki na musamman ga dan majalisar, Jamilu Umar, ya ce, an yi wa masallatan kwaskwarima gaba dayan su.
- Gwamnan Zamfara Ya Kaddamar Da Kwamitin Asusun Samar Da Tallafin Tsaro
- Matsalar Tsaro: Gwamna Dauda Ya Kaddamar Da ‘Askarawan’ Zamfara
Umar, ya ce duk masallatai ashirin din yanzu sun zama na zamani. Haka kuma an gina masallatai sama da 100 na hamsus-salawati da sake gina wasu a yankuna daban-daban a cikin mazabar dan majalisar.
A cewarsa, sake gina masallatai na daga cikin kokarin Dan majalisar na samar da ribar dimokuradiyya ga al’ummar mazabarsa.
A wani labarin kuma, dan majalisar ya mayar da gidansa zuwa cibiyar haddar Alkur’ani Mai girma don yin karatu a ciki.
Dan majalisar har ila yau, ya sake gyara wasu makarantun Islamiyya 14 dan tafiya tare da daukar nauyin kula da kayan makaranta na dalibai da sauran dawainiyar da suka shafi makarantar.
Dan majalisar ya kuma dauki nauyin biyan malaman makarantun Islamiyya na dukkan makarantu 14 da ke cikin Kananan Hukumomin Maru da Bungudu na jihar.
Da yake tsokaci a madadin al’ummar yankin, Muhammed Umar, ya yaba da kokarin da dan majalisar ya yi na ribatar rimin dimokuradiyya da al’ummar mazabarsa suka samu.