Shahararren lauyan nan mai kare hakkin dan adam, Barr. Bulama Bukarti, ya bayyana cewa zaiyi iya yinsa idan har dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso ya hade da na jam’iyyar LP, Peter Obi.
Bulama, wanda kawo yanzu yake zaune a kasar Ingila, ya bayyana hakan ne a shafinsa na sada zumunta na Facebook da yamma cin yau.
A cewar Bulama, indai Kwankwaso da Peter Obi suka hade aka fitar da dan takarar Shugaban kasa da Mataimaki a tsakanin su tabbas zai bada gudunmawa dari bisa dari domin ceto Nigeria.
“Indai Allah Ya taimaki Najeriya, NNPP ta yi nasara wajen hadaka da Labour Party Kwankwaso ya za ma dan takarar NNPP da LP, zan goyi bayan wannan ticket din ta dukkan hanyoyin da zan iya bada gudummuwa. Za mu fito mu yi kamfe iya iyawarmu domin mu ceto kanmu da kasarmu’. In ji Bulama Bukarti.
A satin daya gabata ne Kwankwaso, wanda tsohon gwamnan jihar Kano ne, yayi hira da manema labarai inda yace suna tattauna wa da Peter Obi, wanda shima yake takarar shugaban kasa a karkashin tutar jam’iyyar Labour Party, wato LP.