Jamiyyar NDP ta nemi Sakataren yada labarai na jamiyyar PDP na Kasa, Debo Ologunagba ya gaggauta neman yafiyar Mai Girma Jakadan Nijeriya a Jamhuriyar Benin, Laftanar Janar Tukur Buratai mai murabus.
Bukatar na kunshe ne cikin sanarwar da Sakatare Janar na Jam’iyyar NDP, Dakta Bolaji Abdulkadir ya rabawa manema labarai a garin Abuja.
Dakta Bolaji ya ci gaba da cewa, sanarwar da Debo Ologunagba ya fitar ta labaran kage a kan Buratai wani sabon yunkuri ne na son bata wa Buratai suna, na alakanta Buratai da mallakar wani gida a garin Abuja da hukumar yaki da almundahana da mallakar kadarori ba bisa ka’ida ba (ICPC) ta gano na naira biliyan 1.85.
A cewarsa, fayyace adadin kudaden da hukumar ta yi ya nuna cewa PDP na cikin rudani ne kawai na rashin me ke tafiya a kasar, inda ta Bazama wajen sanar da yan Nijeriya labaran karya.
Debo ya ce, PDP tun bayan rasa kimarta da ta yi a gun ‘yan Nijeriya yanzu ta na son ta tabbatar wa da ‘yan kasar nan har yanzu tana nan, amma ta hanyar yada labaran karya ga ‘yan Nijeriya.
A cewarsa, PDP har yanzu ta na a cikin jin tsoron tunkarar zabubbukan 2023 shi ya sa ta fito da sabon shirin yada labaran karya ga ‘yan Nijeriya.